Kuma dai: Zakanya ta cinye wata budurwa da ta tafi yawon buɗe idanu gidan namun daji

Kuma dai: Zakanya ta cinye wata budurwa da ta tafi yawon buɗe idanu gidan namun daji

Wani mummunan al’amari ya faru a kasar birnin Pretoria na kasar Afirka ta kudu, inda wata mata mai shekaru 22 ta kai ziyarar bude idanu zuwa gidan namun daji, amma wata zakanya ta yi ajalinta.

Wannan lamari mai ban tausayi dai ya faru ne a ranar Laraba 28 ga watan Feburairu, a gidan namun daji dake unguwar Hammanskraal, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

KU KARANTA: Rikicin jihar Kaduna: An banka ma gidajen wani kauye wuta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin hukumar bada agajin gaggawa na 911 na kasar, Nick Dollman yana cewa jami’an hukumarsa sun yi gaggawar kai ma budurwar agaji, bayan da suka samu kira daga jama’an dake wajen.

Kuma dai: Zakanya ta cinye wata budurwa da ta tafi yawon buɗe idanu gidan namun daji
Zakanya

“Matar ta samu munanan raunuka matuka a sassan jikinta, don haka nan take ta mutu.” Inji Kaakakin, haka zalika ya kara da cewa jama’an dake gidan ne suka fara kai mata dauki tun ma kafin su isa.

Idan za’a tuna ko a kwanakin baya sai da wata Zakanya ta kashe mutumin dake kula da ita a gidan namun daji dake cikin wani wajen shakatawa a cikin birnin Kaduna mai suna Gamji park.

Bugu da kari, kimanin shekaru 2 da suka gabata ma sai da wani Zaki ya balle daga gidan namun daji na garin Jos, jihar Filato, wanda rahotanni suka ce ya kwashe sama da shekaru 20 a gidan, inda aka kira Sojoji suka bindige shi don gudun kada ya tafka ta’asa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng