Kada ya cinye wani fasto yayin da yake yi wa mabiyansa wankan tsarki a kogi

Kada ya cinye wani fasto yayin da yake yi wa mabiyansa wankan tsarki a kogi

- Wani kada ya yi ajalin wani Fasto a kasar Habasha

- Kadan ya cafke faston ne yayin da yake yiwa wasu mabiyansa wankan tsarki a wani tafki

- Masunta sunyi kokarin ceto faston amma abin ya ci tura

Wani kada ya halaka wani fasto a yayin da yake yi wa wasu mabiyansa wankan tsarkin addinin kirista a wani kogi da ke kudancin Habasha.

Fasto Docho Eshete yana yi wa wasu mutane 80 wankan tsarkin ne a safiyar ranar Lahadi a Tafkin Abaya da ke Arba Minch a gundunmar Merkeb Tabya.

Kada ya cinye wani fasto yayin da yake yi wa mabiyansa wankan tsarki a kogi
Kada ya cinye wani fasto yayin da yake yi wa mabiyansa wankan tsarki a kogi

KU KARANTA: Talauci ya sanya na sayar da jariri na kan kudi N670,000 - Wata matashiya 'yar shekaru 17

Mazauna garin da jami'an Yan sanda sun shaidawa BBC Amharic cewa kadan ya sulalo daga cikin ruwan ne kuma ya cafke faston yayin da yake yiwa wani wankan tsarkin.

Fasto Docho ya riga mu gidan gaskiya sakamakon cizon da kadan ya yi masa a bayansa da hanayensa da kafafuwansa.

"Ya kammala yi wa mutum na farko wankan, ya zo kan na biyu kawai sai wani kada ya fito daga tafkin ya damko fasto," kamar yadda wani wanda abin ya faru a idanunsa a garin Ketema Kairo ya fada.

Duk da namijin kokarin da masunta da mazauna unguwar su kayi don ceto rayuwar Docho, hakan bata yiwu ba, inji wani dan sanda mai suna Eiwnetu Kanko.

Sai dai masuntar sunyi amfani da ragar kamun kifi wajen hana kadar nutsar da gawan faston kasar kogin.

Kazalika, kadan ya gudu ba tare da masuntan sun sami damar halaka shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel