Yan Daba Sun Lalata Ofishin Yakin Neman Zaben APC a Jihar Kogi

Yan Daba Sun Lalata Ofishin Yakin Neman Zaben APC a Jihar Kogi

  • Wasu ƴan daba sun lalata ofishin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi
  • Ƴan daban waɗanda ba a san ko su wanene ba, sun lalata ofishin ne a ƙaramar hukumar Dekina ta jihar
  • Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta nesanta kanta daga lalalta ofishin inda ta ce magoya bayanta masu son zaman lafiya ne

Jihar Kogi - Wasu ƴan daba sun lalata ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dekina ta jihar Kogi.

Mista Kingsley Fanwo, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na gwamnan jihar Kogi ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 22 ga watan Satumba, cikin wata sanarwa da ya fitar a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, cewar rahoton PM News.

Yan daba sun lalata ofishin APC a Kogi
Yan daba sun lalata ofishin jam'iyyar APC a jihar Kogi Hoto: PMNews.com
Asali: UGC

A kalamansa:

Kara karanta wannan

Atiku/Obi vs Tinubu: "Na Hango Hukuncin", Babban Malamin Addini Ya Bayyana Hukuncin Da Kotun Koli Za Ta Yanke

"Muna kira da jawo hankalin jama’a da jami’an tsaro cewa wasu ƴan daba sun lalata ofishin yaƙin neman zaɓen mu da ke ƙaramar hukumar Dekina."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna yaba wa al'ummar Kogi ta Gabas saboda goyon bayansu ga ɗan takarar mu, wanda ke son haɗin kan jiharmu da cigabanta."

Sai dai, Fanwo, ya buƙaci magoya bayan jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Dekina da su guji yunƙurin ɗaukar fansa ko da kuwa an tsokale su da faɗa, inda ya ce jam'iyyar APC goyon bayan zaman lafiya take yi.

Ya yi iƙirarin cewa ɗan takarar Gwamna na APC, Usman Ododo, ya samu karɓuwa sosai a faɗin jihar.

Ya bayyana cewa ɓangaren shari'a na jam'iyyar na tattara cikakken rahoto, bayan an gabatar da rahoton farko.

Ko a akwai hannun jam'iyyar SDP?

Da aka tuntuɓi sakataren jam’iyyar SDP na jihar, Dr Arome Okeme, ya musanta cewa akwai hannun jam'iyyarsu a ciki, inda ya ƙara da cewa wannan wani tuggun APC ne na ɓata sunan jam'iyyar SDP.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Babban Likita Da Ake Ji Da Shi a Jihar Arewa

Okeme ya ce SDP da magoya bayanta masu son zaman lafiya ne, sannan ya ƙara da cewa suna da ƙwarin gwiwar cewa nasara ta su ce a zaɓen gwamnan na ranar 11 ga watan Nuwamba.

Yan Daba Sun Farmaki Jigon SDP a Kogi

A wani labarin kuma, ƴan daba sun kai farmaki gidan wani jigo a jam’iyyar SDP, Abdul Yusuf Amichi, wanda aka fi sani da Abdul limbo, da ke Ugwolawo, karamar hukumar Ofu a jihar Kogi.

Rahotanni sun nuna cewa a yayin wannan harin yan daban sun banka wa motar ɗan siyasan wuta a gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel