Miyagun 'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Tsaro Uku a Jihar Edo

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Tsaro Uku a Jihar Edo

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi ajalin jami'an tsaron ESSN yayin da suke kan aiki a jihar Edo ranar Alhamis da daddare
  • Rahotanni sun bayyana cewa kisan na da alaka da rikicin shugabanci da ke faruwa a yankin Okhun, ƙaramar hukumar Ovia
  • Rundunar 'yan sanda ta ce har yanzu babu wanda ya kai mata rahoto kan lamarin amma wani jami'in tsaro ya tabbatar

Jihar Edo - Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba a tantance ko su waye sun halaka jami'an tsaron rundunar Edo State Security Network da ke ƙarƙashin gwamnatin jihar ranar Alhamis da daddare.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa 'yan bindigan sun harbe jami'an tsaron su uku a yankin Okhun da ke ƙaramar hukumar Ovia ta Arewa maso Yamma a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Babban Malami da Wasu 2 a Babban Birnin Jihar APC

Yan bindiga sun kai hari Edo.
Miyagun 'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an Tsaro Uku a Jihar Edo Hoto: punchng
Asali: Twitter

Vanguard ta tattaro cewa kisan jami'an tsaron na da nasaba da rikicin shugabanci a yankin da kuma ramuwar gayya na kungiyoyin asiri.

Wasu ganau sun bayyana cewa maharan su kusan 10 sun shiga ƙauyen kana suka bindige jami'an rundunar ESSN har lahira suna kan aikinsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ya faru

A wani faifan bidiyo da ake yaɗawa, wani mamban rundunar tsaron ESSN wanda ya bayyana kansa da "Kwamanda Small Baba" ya ce ya tsallake rijiya da baya ta hannun wasu mutane.

Jami'in wanda ya ji raunuka a hannun damansa, ya bayyana cewa wasu masu kawo agaji ne suka taimaka masa ya tsira daga maharan.

“A yau (daren Alhamis), mun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a yankin Okhun. Nan take muka nufi yankin bayan samun bayanin abin da ke faruwa."

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Jami'an Tsaro da Mutanen Gari Sun Halaka 'Yan Bindiga Sama da 20 a Jihar Arewa

"Amma ‘yan bindiga suka farmake mu, suka kashe mutane na guda uku, ni ma suka harbe ni yayin wannan farmaki, amma na yi nasarar tserewa.”

Wane mataki aka ɗauka kan lamarin?

Da aka tuntuɓe mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor, ya ce har yanzun rahoto bai riske shi ba amma zai tuntubi DPO na yankin kafin ya ce komai.

Akwai Alamun Tambaya Kan Wasu Yan Siyasa Game da Kashe-Kashen Filato, Mutfwang

A wani labarin na daban Gwamnan jihar Filato, Celeb Mutfwang, ya tona waɗanda yake zargi da hannu a ta'addancin da ake aikata wa a jiharsa.

Ya ce akwai wasu 'yan siyasa da yake ganin ya kamata a titsiye su amsa tambayoyi kan alaƙarsu da 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel