Yan Sanda Sun Sha Alwashin Hukunta 'Yan Luwadin da Aka Kama a Jihar Delta

Yan Sanda Sun Sha Alwashin Hukunta 'Yan Luwadin da Aka Kama a Jihar Delta

  • Hukumar 'yan sanda a jihar Delta ta lashi takobin hukunta baki ɗaya 'yan luwaɗi sama da 100 da ta kama a Otal
  • Rahoto ya bayyana cewa jami'an yan sanda sun kama waɗanda ake zargin 'yan luwaɗi ne yayin da suke bikin auren jinsi
  • Haka nan hukumar ta ce dakarunta sun baza koma suna bibiyar wasu 'yan bindiga da suka yi ajalin jami'inta guda ɗaya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Delta state - Rundunar ‘yan sandan reshen jihar Delta ta sha alwashin gurfanar da wadanda ake zargi da hannu wajen shirya bikin auren ‘yan luwadi.

Jaridar Leadership ta ce akalla mutane 100 da ake zargin 'yan luwadi ne aka cafke a wurin daurin auren a lokacin da wata tawagar jami'an 'yan sanda ta kai samame wurin.

Hukumar yan sanda ta kama 'yan luwaɗi a Delta.
Yan Sanda Sun Sha Alwashin Hukunta 'Yan Luwadin da Aka Kama a Jihar Delta Hoto: leadership
Asali: UGC

Rundunar 'yan sandan ta ce zata gurfanar da 'yan luwaɗin a gaban Ƙotu ne bisa hujjar dokar Najeriya da ta haramta auren jinsi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Ɗalibin Jami'an Ya Soka Wa Budurwarsa Wuƙa Har Lahira Kan Abu 1

Hukumar 'yan sandan ta sha wannan alwashi ne a lokacin da ta nuna 'yan luwaɗin da aka kama a wani shahararren otal da ke kan titin Refinery, Ekpan a karamar hukumar Uvwie, jihar Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan sanda sun nuna waɗanda ake zargin ne a hedikwatar ‘yan sanda ta Ekpan da ke yankin Uvwie gabanin gurfanar da su a gaban kotu.

Jami'an 'yan sanda sun bazama neman 'yan bindiga

Haka nan kuma rundunar ‘yan sandan ta ce tana bibiyar wasu ‘yan bindiga da suka kashe ɗan sanda da ke aiki a caji ofis ɗin Isiokolo (Otoro-Agbon), karamar hukumar Ethiope ta Gabas a jihar Delta.

An harbe dan sandan ne a lokacin da ‘yan bindigar su biyu aƙalla suka isa kofar shiga ofishin 'yan sandan, suka bude wuta kan mai uwa da wabi, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: An Kama 'Yan Luwaɗi Sama da 100 Suna Bikin Auren Jinsi a Jiha 1 a Najeriya

‘Yan sanda biyu suka samu raunuka daban-daban a yayin harin kuma nan take aka garzaya da su asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwar jami'i guda ɗaya.

Dalibin Jami'ar UNIFORT Ya Daba Wa Budurwarsa Wuƙa Har Ta Mutu

A wani rahoton na daban kuma Jami'an 'yan sanda reshen jihar Edo sun damƙe wani ɗalibain jami'a bisa zargin halaka budurwarsa.

Kwamishinan 'yan sanda ya ce nan bada daɗewa ba za a gurfanar da shi a gaban Kotu bisa tuhumar aikata kisan kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel