Gwamna Dikko Radda Na Katsina Ta Tube Wani Masaraucin Gargajiya Na Kauyen Kuraye A Jihar

Gwamna Dikko Radda Na Katsina Ta Tube Wani Masaraucin Gargajiya Na Kauyen Kuraye A Jihar

  • Gwamnatin jihar Katsina ta amince da korar wani masaraucin gargajiya a jihar kan zargin jagorantar daurin aure ba bisa ka’ida ba
  • Wanda aka tube Alhaji Abdullahi Abubakar shi ne Sarkin Kurayen Katsina a karamar hukumar Chiranchi inda gwamnan jihar ya fito
  • Sakataren masarautar Katsina, wanda shi ne Sarkin Yakin Katsina, Alhaji Bello Ifo shi ya bayyana haka a jiya Litinin 18 ga watan Satumba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Katsina – Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya tube wani mai rike da sarautar gargajiya Alhaji Abubakar Abdullahi na kauyen Kuraye a cikin jihar.

Sakataren masarautar Katsina, wanda shi ne Sarkin Yakin Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo shi ya bayyana haka a jiya Litinin 18 ga watan Satumba.

Gwamnatin Katsina ta tube sarkin Kuraye a sarauta
Gwamnatin Katsina Ta Tube Wani Masaraucin Gargajiya. Hoto: Umaru Dikko Radda.
Asali: Facebook

Yaushe Dikko Radda ya kori masaraucin?

Legit ta tattaro cewa Ifo ya ce ya bayyana cewa wannan umarni ya fito ne daga gwamnatin jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Zuba Yayin Da Dan Majalisa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya A Yau Dinnan, Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Wannan wasika daga Mai Martaba Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman ya karbe ta ne daga Sakataren Gwamnatin jiha a ranar 15 ga watan Satumba.
“Wanda ke da alaka da auren Alhaji Lawal Mamman Auta da kuma Hajiya Halimatu Abdullahi Kuraye inda gwamnatin jihar Katsiya ta bukaci ka ajiye mukamain Sarkin Kurayen Katsina.
“A dalilin haka, masarautar Katsina ta tube ka mukamin Sarkin Kurayen Katsina daga yau Litinin 18 ga watan Satumba.”

Kuraye kauye ne da ke cikin karamar hukumar Chiranchi inda gwamna jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya fito.

Meye dalilin Dikko Radda na tube sarkin?

Hadimin gwamnan a bangaren yada labarai, Isa Miqdad ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter.

Wannan mataki kamar yadda rahotanni su ka tabbatar nada alaka da daurin aure da mai sarautar gargajiyar ya jagoranta wanda ke dauke da matsaloli.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Sauraran Korafe-korafen Zabe Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Da Ake Na Gwamnan jihar Arewa

Ana zargin Abubakar Abdullahi da jagorantar aure wanda ba a yi gwajin lafiya ba kuma a karshe aka fahimci daya na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da sabon rabon kayan tallafi

A wani labarin, Gwamnatin jihar Katsina a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba ta kaddamar da rabon tallafi a karamar hukumar Kankara ta jihar.

Wannan na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur wanda hakan ya sanya tsadar rayuwa da tashin kayan kayan abinci da sauran kayan masarufi ya karu a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel