Bayan Soyayyar Shekaru 2, Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ba Ya Dukanta

Bayan Soyayyar Shekaru 2, Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ba Ya Dukanta

  • Wata budurwa a Najeriya ta rabu da saurayinta yayin da aka wallafa sakwannin hirar da su ka yi da shi a manhajar ‘WhatsApp’
  • A cikin hirar, budurwar ta fada wa saurayin cewa ya gagara kawata soyayyarsu da wasu abubuwa daban kamar duka
  • Ta ce ita a rayuwarta ta fi son saurayin da zai na dukanta da kuma daure ta amma shi kuma ya ki shiyasa ta rabu da shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ta nemi rabuwa da saurayinta bayan shafe tsawon lokaci su na soyayya saboda ya ki cin zarafinta lokacin da su ke tare.

A wani sakon ‘WhatsApp’ da aka bankado wanda ya wallafa a shafin Twitter, budurwar ta bayyana cewa ta na son ana dukanta, Legit ta tattaro.

Budurwa ta rabu da saurayinta sabda ya ki dukanta
Budurwa Ta Bayyana Dalilin Rabuwarta Da Saurayinta Bayan Soyayyar Shekaru 2. Hoto: Twitter/@ustinangelo/Getty Images/Valeriia Titarenko. An yi amfani da hoton don misali ne kawai.
Asali: UGC

Meye saurayin ke cewa kan budurwar?

Saurayin mai suna @ustinangelo ya yi mamakin wannan abin da budurwar ta fada inda ya ke tunanin ko aljanu ne su ka kamata.

Kara karanta wannan

“Maza Guduna Suke Yi”: Budurwa Mai Katon Hanci Ta Koka, Ta Zubar Da Hawaye Saboda Rashin Mashinshini

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma budurwar ta ce ita ta fi son soyayyarsu ta kasance da wasu abubuwa kamar duka da kuma yada al’amuran soyayyarsu ga jama’a.

Ta kuma fada wa saurayin da ya fara daureta inda shi kuma ya ke kin wannan bukata tata a duk lokacin da ta nemi hakan.

Ta ce:

“Duk lokacin da na yi magana a kai, sai ka na kaucewa maganar, ba ka damu da damuwa ta ba ko kadan shi yasa.”

Saurayin ya wallafa lamarin inda ya ce:

“Jiya ban yi bacci sosai ba, na shiga damuwa, na yi kokarin gyara al’amura amma lambarta ya ki shiga.”

Mutane da dama sun yi martani inda su ka shawarci saurayin da ya yi watsi da budurwar ta shi.

Martanin mutane kan lamarin budurwar da saurayinta:

@BossWhyt:

Kara karanta wannan

“Kana Da Kyau”: Wata Uwa Ta Roki Kyakkyawan Saurayi Da Ya Taimaka Ya Auri Diyarta

“Karanta irin wannan ya na ba ni dariya, ya kamata ma su rin wannan tunani su auri juna, ba za ka taba sauya mutane ba idan kasan haka ka huta.”

@Ishow_leck:

“Da farko idan ta nemi haka, ka kore ta, za ta samu abin da ta ke so a gaba, dukkan abubuwan za ta same su, damuwa na shi ne lokacin da ta bukaci hakan ba ka yi mata ba. Ka na tunanin za ka kaucewa irin haka a wurin mata, za su samu a wani wuri idan har su na so.”

Budurwa Ta Biyan Kudin Haya N500k, Ashe An Siyar Da Gidan

A wani labarin, wata budurwa 'yar Najeriya ta sha mamaki yayin da ta biya kudin haya bayan an siyar da gidan.

Budurwar ta ce ta ba da kudin bayan an siyar da gidan ashe mai gidan ya dade da tsallakawa kasashen ketare.

Ta ce ta biya Naira dubu 500 ga mai gidan a rashin sani inda ta nemi mai gidan ta rasa sama da kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel