Hisbah Ta Tama Mutumin da Ya Kashe Jaririyar Da Matarsa Ta Haifa a Kano

Hisbah Ta Tama Mutumin da Ya Kashe Jaririyar Da Matarsa Ta Haifa a Kano

  • Dakarun Hisbah sun kama wani matashin magidanci bisa zargin kashe ɗiyarsa 'yar kwana ɗaya da haihuwa a jihar Kano.
  • Mutumin mai suna, Musbahu Salisu, ya amsa laifinsa ya ce burinsa ya samu ɗa namiji amma sai natarsa ta haifi mace
  • Mataimakin kwamandan Hisbah ya ce zasu miƙa wanda ake zargi ga sashin binciken masu aikata muggan laifuka (CID)

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wani magidanci ɗan shekara 28 a duniya da ke zaune a ƙauyen Doka, karamar hukumar Tofa ta jihar Kano, Musbahu Salisu, ya shiga hannun jami'an Hisbah.

Jami'an hukumar 'yan sandan Musulunci ta jihar Kano watau Hisbah sun kama mutumin ne bisa zargin halaka ɗiyarsa mace da matarsa ta haifa kwana ɗaya da haihuwarta.

Jami'an hukumar Hisbah na jihar Kano.
Hisbah Ta Tama Mutumin da Ya Kashe Jaririyar Da Matarsa Ta Haifa a Kano Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa guba ya zuba a shayi sannan ya shayar da jaririyar awanni bayan ta baro cikin mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Ɗalibar Jami'ar Tarayya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Kasuwa

Meyasa mutumin ya aikata wannan ɗanyen aikin?

A cewarsa, ya jima yana marari da fatan samun ɗa namiji amma abin takaici matarsa ta santalo ɗiya mace, wanda hakan ya sa ya aikata wannan ɗanyen aikin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A rahoton The Cable, Musbahu ya ce:

"Na fi son ɗa namiji amma matata ta haifi mace, wanda hakan ya sa na kashe jaririyar. Bayan ta haihu lafiya, na je na siyo Fiya-Fiya na zuba a shayi, ba baiwa jaririyar ta sha kuma ta mutu."

Magidancin ya ƙara da cewa ya bai wa matarsa mahaifiyar jaririyar, Sa'adatu Musbahu, kwayoyi saboda ta yi bacci ta yadda zai aikata abin da ya zo ba tare da saninta ba.

"Lokacin da zan siyo gubar, na haɗo da maganin bacci. Na ba matata ta kama bacci sa'ilin da nake shayar da jaririyar shayi mai guba."

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Daga Ba Shi Wurin Zama, Malami Ya Ɗirka Wa Matar Abokinsa Ciki

A nasa jawabin, mataimakin kwamandan Hisbah mai kula da sashin ayyuka, Mujahid Aminudeen, ya ce Musbahu ya amsa aikata laifin kuma zasu mika shi ga CID don ɗaukar mataki.

Ya kara da cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta tsaftace Kano daga duk wani nau’i na munanan dabi’u domin gina al’umma mai ɗa'a.

Mutane Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Sabon Hari A Jihar Kaduna

Rahotanni sun nuna cewa 'Yan bindiga sun kai sabon kazamin harin kan mutane a ƙauyen Dogon Noma-Unguwan da ke karamar hukumar Kajuru a Kaduna.

Bayanai sun nuna maharan sun halaka mutane biyu kuma sun yi garkuwa da wasu mutum uku yayin harin na ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel