“Diyata Mutum Ce”: Mahaifiyar Kyakkyawar Yarinya Mai Kama Da Yar Tsana Ta Magantu a Bidiyo

“Diyata Mutum Ce”: Mahaifiyar Kyakkyawar Yarinya Mai Kama Da Yar Tsana Ta Magantu a Bidiyo

  • Wata uwa ta saki hadadden bidiyon kyakkyawar diyarta wacce mutane kan zata yar tsana ce
  • Yayin da take sakin bidiyon a shafinta na TikTok, matar ta yi jawabi ga wadanda su kan kira kyakkyawar diyarta da ta bogi
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun garzaya sashinta na sharhi don bayyana ra'ayinsu game da yarinyar

Wata uwa ta yi martani ga martani mara dadi da take samu daga jama'a game da diyarta.

Mutane da dama da suka ci karo da hotunan yarinyar a Instagram sun ce lallai yarinyar ba mutum bace, cewa yar tsana ce.

Uwa da diyarta mai kama da yar tsana
“Diyata Mutum Ce”: Mahaifiyar Kyakkyawar Yarinya Mai Kama Da Yar Tsana Ta Magantu Hoto: @badgal.abbey/TikTok
Asali: TikTok

Wata uwa ta yi jawabi ga masu kiran diyarta da yar tsana

A cikin bidiyon, ta yi watsi da ikirarin yayin da ta nuna wa duniya kyakkyawar diyarta mai jini a jika da kamanni mai ban mamaki.

Kara karanta wannan

“Maza Guduna Suke Yi”: Budurwa Mai Katon Hanci Ta Koka, Ta Zubar Da Hawaye Saboda Rashin Mashinshini

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take yada bidiyon, ta yi jawabi ga masu kiran diyarta da na bogi sannan ta bukace su da su daina yin irin wannan ikirarin.

Uwar yarinyar ta ce:

"Wato sun wallafa hotunan diyata a wasu shafuka sannan mutane da dama suna ta fadin ne yasa za a wallafa hoton yar tsana. Kuma zan kasance karkashin martaninsu ina fadin wannan diyata ce a gaske."

Martanin jama'a yayin da wata uwa ta saki bidiyon diyarta mai kama da yar tsana

@mzzzz..pweedy ta ce:

"Ta yi kama da yar tsana. Tana da kyau."

@shevonnejohnson45 ta rubuta:

"Gaskiya ta yi kama da yar tsanar gaske. Kyawu tsantsa."

@kentuckyokc ta ce:

"Wayyo Allah tana da kyawu tsantsa na tayaki murna kyakkyawar uwa."

@suzywitdauzi0 ta yi martani:

"Nima na ji shi amma idanunta suna da girma sosai sai na ce ta gaske ce."

Kara karanta wannan

“Kana Da Kyau”: Wata Uwa Ta Roki Kyakkyawan Saurayi Da Ya Taimaka Ya Auri Diyarta

@sharondeshay ta ce:

"Wayyo Allah ta yi kama da yar tsana! muna kiran jikata da mai kama da yar tsana saboda tana kama da babin roba ita ma! kyakkyawar yarinya."

Kalli bidiyonta a kasa:

Matashiya ta koka saboda rashin saurayi, ta ce maza na gudunta saboda hancinta

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa ta koka saboda ta gaza samun saurayi duk da tana burin mallakar guda daya.

Matashiyar ta wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok, Ammie Sweeshy, ta koka sosai cewa babu wanda ke sonta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel