Tallafin Fetur: Daga Dawowa Yajin Aiki, Ma’aikata Su Na Tunanin Sake Rufe Ofisoshi

Tallafin Fetur: Daga Dawowa Yajin Aiki, Ma’aikata Su Na Tunanin Sake Rufe Ofisoshi

  • ‘Yan kwadago da kungiyoyin ma’aikata za su iya tafiya jajn aikin da zai shafi ko ina a Najeriya
  • Shugabannin NLC sun zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawarin da aka yi da ita a farkon wata
  • Idan wa’adin da aka ba gwamnati ya kare ba tare da daukar matakai ba, dole za a koma gidan jiya

Abuja - Ba su dade da dawowa aiki ba, sai aka sake jin labari kungiyoyin ma’aikata, ‘yan kasuwa da na kwadago za su iya komawa gidan jiya.

A ranar Talata aka ji ‘yan kwadagon su na barazanar shiga yajin-aiki idan gwamnatin tarayya ba ta biya mata bukatun da ta gabatar ba.

Kwanaki 21 da ma’aikatan su ka bada ya kusa shudewa, nan da mako guda wa’adin zai kare.

'Yan kwadago
NLC: 'Yan kwadago su na zanga-zanga Hoto: www.nlcng.org
Asali: UGC

Janye tallafin man fetur

Kara karanta wannan

Shari’ar zabe, 50% da Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Zabe – Ministan Jonathan

‘Yan kwadagon ba su gamsu da yadda gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur ba tare da an kammala tsare-tsaren da za su rage radadi ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kungiyoyon ma’aikatan sun ce yajin-aikin ya zama dole tun da gwammnatin Bola Tinubu ba ta dauki abin da gaske ba, ta bari ana shan wahala.

Rahoton yake cewa yajin-aikin zai iya jawo abubuwa su tsaya cak, kuma zai dauki dogon lokaci, wanda hakan zai taba tattalin arzikin kasar nan.

Muddin hakan bai samu ba, ‘yan kwadago sun sha alwashin tafiya yajin-aikin da sai baba ya gani.

Shugabannin NLC sun taba Tinubbu

Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce shugaban kasa ya yi alkwarin yi wa kwamitinsa kwaskwarima, abin da bai iya yi ba har zuwa makon nan.

Mataimakin sakataren NLC, Christopher Onyeka, ya ce ba daidai ba ne a ba talakawa buhun shinkafa guda, amma ‘dan majalisa ya samu N100m.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Tayi Karin Haske a Kan ‘Shirye-Shiryen’ Kirkiro Sababbin Haraji

A cewar Onyeka, gwamnatin tarayya ta warewa ‘yan majalisar tarayya N70bn alhali mafi yawan mutanen kasar nan su na rayuwa cikin wahala.

"Gwamnatin tarayya ta na sayen gidaje da motoci na fiye da N100m ga kowane ‘dan majalisa, amma duk an yi shiru.
Mutanen Najeriya sun yi tsit tamkar ana yin abin da ya kamata ne. NLC ta na kira ga ‘Yan Najeriya su hada-kai tare."

- Christopher Onyeka

"A jira Tinubu ya dawo gida"

A ranar 1 ga Satumban nan, kungiyoyin su ka fadawa gwamnati cewa sun ba ta makonni uku domin ganin an kawowa mutanen kasar sa'ida.

Rahoto ya zo cewa Simon Lalong ya yi alkawari da zaran shugaba Bola Tinubu ya dawo daga Indiya, za a warware matsalolinda aka samu da NLC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng