Kamfanin Wutar Lantarki Ya Sanar Da Gyara Wutar Lantarki A Najeriya

Kamfanin Wutar Lantarki Ya Sanar Da Gyara Wutar Lantarki A Najeriya

  • Kamfanin samar da wutar lantarki a Najeriya ta tabbatar da gyara wutar da ta baci a safiyar yau
  • Kamfanin ya sanar da haka a shafinsa na Twitter a yau Alhamis 14 ga watan Satumba inda ya bai wa mutane hakuri
  • Wannan na zuwa ne bayan shafe fiye da sa'o'i 12 babu wutar wanda hakan bai taba faruwa ba cikin shekara daya

Bayan shafe fiye da sa'o'i 12 babu wuta a fadin Najeriya baki daya, yanzu wutar ta dawo.

Wannan na zuwa bayan dauke wutar a fadin kasar baki daya wanda aka shafe kusan shekara ba a samu irin haka ba, TheCable ta tattaro.

An gyara wutar lantarki a Najeriya
Kamfanin Wutar Lantarki Ya Sanar Da Gyara Wuta A Najeriya. Hoto: The Glitters.
Asali: UGC

Yaushe aka gyara wutar a Najeriya?

Kamfanin samar da wutar lantarki a Najeriya (TRCN) ta tabbatar da samun matsalar a yau Alhamis 14 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Yadda Bindigar Tashar Kainji/Jebba Ta Jefa Miliyoyin ‘Yan Najeriya Cikin Duhu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A safiyar yau Alhamis ne dai aka waye gari babu wuta duk Najeriya inda rahotanni su ka ce an dauke wutar da misalin 12:40 na dare.

Kamfanin samar da wuta na Eko Disco ya tabbatar cewa a yanzu an gyara wutar kuma ta dawo a Najeriya, cewar Al-Jazeera

Kamfanin ya bayyana haka ne a shafin Twitter a yau Alhamis 14 ga watan Satumba, cewar Punch.

A cikin sanarwar ya ce:

"Ya ku kwastomomi masu daraja ku sani a yanzu an gyara wutar Najeriya kuma ta dawo, mun gode da hakurinku."

Meye ne dalilin lalacewar wutar?

Gwamnatin tarayya ta ce matsala aka samu a tashar Kainji, hakan ya yi sanadiyyar da aka fuskanci rashin lantarki.

Ministan harkokin wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi karin haske a jeringiyan bayanai da ya fitar a shafin Twitter a yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Yadda Dakarun Sojoji Suka Kama Makashin Dorathy Jonathan a Kudancin Kaduna

Ministan ya bayyana yadda tashar Kainji ta jawo wutan lantarkin kasar ya durkushe, aka rasa komai, wannan ya jawo ko ina ya zama duhu.

Bayanan Adebayo Adelabu sun zo kenan sai aka samu labari an kama hanyar gyara wutan, a ra'ayinsa nan da shekara guda za a gyara wuta.

An dauke wutar lantarki a Najeriya

A wani labarin, Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauke wutar lantarki gaba daya a fadin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Alhamis 14 ga watan Satumba a gaba daya fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel