Dalar Amurka Ta Koma N930 Yayin da CBN Ya Karyata Shirin Maida $1 Ta Zama N1.25

Dalar Amurka Ta Koma N930 Yayin da CBN Ya Karyata Shirin Maida $1 Ta Zama N1.25

  • Babban bankin Najeriya ya ce rahoton da ya ke yawo na karfafa Naira a kan Dala ba gaskiya ba ne
  • Ana rade-radin cewa za ayi kokarin ganin $1 ta koma N1.25, daga ji an san hakan da kamar wahala
  • Yanzu haka an saida Dalar Amurka a kan N930, mafi arahar da Naira tayi kenan na tsawon kwanaki

Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN ya karyata wani rahoto da yake yawo cewa akwai yunkurin da ake yi domin karya Dalar Amurka.

Legit ta samu labari ana yada jita-jita a kafofin sadarwa na zamani cewa Dala za ta koma N1.25 kobo a sakamakon wani tsari da za a kawo.

A ranar Laraba, bankin ya musanya wannan zance mara tushe, ya ce babu yunkurin da ake yi a yanzu na canza kudi ko makamancin hakan.

Kara karanta wannan

Tiriliyan 87 Na Bashin Najeriya, Tinubu Ya Gaza Tabuka Komai, An Bayyana Wadanda Ke Bin Kasar Bashi

Dalar Amurka
Naira 930 ne daidai da Dalar Amurka 1 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

CBN: "N1.25 = $1 ba gaskiya ba ne"

Babban bankin ya fitar da jawabi a dandalin X, ya ce abin da ake yawo da shi ba gaskiya ba ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Bankin CBN na Najeriya zai so ya ja hankalinku game da wannan sako da yake yawo a kafofin sadarwa na zamani, ba gaskiya ba ne, ayi watsi da shi."

- CBN

The Cable ta ce an saidawa ‘yan kasuwa Dalar Amurka a farkon makon nan ne a kan N742.10 yayin da ake cigaba da fama da wahalar Dala a kasar.

Nawa Dala ta ke a zahiri?

Wani ma’aikacin banki ya fada mana su na saye da saida Dala a kan N774-N776 a jiya.

Legit ta yi bincike a ranar Laraba, ta gano cewa farashin da ake saida Dala a bankuna ya sha bam-bam da yadda yake a kafar I & E da CBN ta fito da shi.

Kara karanta wannan

Ana Binciko Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7 a CBN

A kasuwar canji kuwa, darajar Naira ta kara lalacewa domin an saida Dalar Amurka a kan N930 bayan wani hobbasa da aka samu a kwanakin baya.

Da mu ka tuntubi wani ‘dan kasuwar canji da safiyar Alhamis, ya fada mana su na sayen Dala a kan N910, sai daga baya kuma farashin ya sake tashi.

A jihar Kaduna, ‘yan canji sun saye Dala a kan N920 kafin a rufe kasuwa jiya, masu bukatar saye kuwa sai sun biya N930 kafin su iya samun Dala guda.

Binciken Godwin Emefiele a CBN

Ku na da labari cewa lambar wasu makusantan Mista Godwin Emefiele ta fito a wani bincike da ake yi domin bin diddikin asusun babban banki na CBN

Bola Ahmed Tinubu ya dauko hayar tsohon shugaban FRC, Jim Obazee, ya ba shi wannan aiki, kwamitinsa ya fara bankado badakalar Naira tiriliyan 7.

Asali: Legit.ng

Online view pixel