Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in FRSC Har Lahira A Abuja

Direban Babbar Mota Ya Murkushe Jami'in FRSC Har Lahira A Abuja

  • Jimami yayin da direban babbar mota ya yi sanadin jami'in hukumar FRSC a yau Talata 12 ga watan Satumba a kan hanyar Abuja-Kaduna
  • Jami'in hukumar FRSC din ya shiga motar ce don bin umarni bayan an bukaci ya kai motar ofishinsu yayin da direban ya wurgo shi waje
  • Direban da karen motarsa sun tunkudo jami'in waje lokacin da motar ke tsananin gudu, lamarin da ya jawo asara

FCT, Abuja - Wani direban babbar mota ya yi ajalin jami'in Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Marigayin mai suna Idris Hamisu ya rasu ne a yau Talata 12 ga watan Satumba a kokarin bin umarnin shugabanninsa na kai motar zuwa ofishinsu.

Jami'in FRSC ya mutu bayan babbar mota ta murkushe shi
Jami'in FRSC Da Direban Babbar Mota Ya Murkushe Har Lahira A Abuja. Hoto: @ZagazOlaMakama.
Asali: Twitter

Ta yaya jami'in FRSC ya rasa ransa a bakin aiki?

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

Rahoton ZagazOlaMakama shi ya bayyana haka a shafinsa na Twitter a yau Talata 12 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce jami'in FRSC din ya rasa ransa ne bayan direban da yaron motarsa sun wurgo jami'in waje daga cikin motar.

An ce direban ya turo marigayin ne cikin rashin tausayi lokacin da motar ke cikin tsananin gudu marar misaltuwa.

Wane umarni jami'in FRSC ya bi na kai mota ofishinsu?

An umarci jami'in na FRSC ya kai motar zuwa ofishinsu don tsare motar saboda saba doka da mai motar ya yi.

Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun irin haka tsakanin jami'an FRSC da kuma direbobi musamman na babbar mota.

A Najeriya, jami'an tsaro na fuskantar irin wannan lamari, duk da su ma suna yin sanadin wasu jama'ar da basu ji ba basu gani ba.

Kara karanta wannan

Gowon, Akeredolu Da Wasu Fitattun Yan Najeriya 4 Da Aka Yi Karyan Sun Mutu

Direban Babban Mota Ya Halaka Jami'in FRSC a Jihar Kano

A wani labarin, wani direban babbar mota da ba a san ko wanene ba ya kashe jami'in hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC, a kan babban titin Hotoro a jihar Kano.

An gano cewa lamarin ya faru ne a yayin da jami'in na FRSC ya yi yunkurin bincika babbar motan.

Wani shaidan ganin ido mai suna Abubakar Abubakar ya ce an turo jami'in ne ya fado kasa a yayin da ya ke duba motar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel