Kotu Ta Jadada Ikon Da Jami'an FRSC Ke Da Shi Na Kwace Motoci Da Cin Tarar Masu Saba Dokokin Tuki

Kotu Ta Jadada Ikon Da Jami'an FRSC Ke Da Shi Na Kwace Motoci Da Cin Tarar Masu Saba Dokokin Tuki

  • Hukumar FRSC ta kara samun karfi daga kotu inda hukumar ta kara samun tabbacin cin taran masu abin hawa
  • Wannan hukunci ya biyo bayan shigar da kara da wani lauya ya yi kan cin zarginsa da hukumar ta yi
  • Lauyan ya bukaci kotun ta tilasta hukumar biyansa N10m kan barnar da aka yi masa, madadin haka kotun ta ba wa hukumar N50,000

FCT, Abuja - Kotu ta karawa Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) karfi don kama motoci da kuma cin taran wadanda suka karya dokar tuki.

Hukumar ta kama wani lauya dan jihar Akwa Ibom, Michael Benson a shekarar 2017 kan zargin rashin lasisin tuki da rashin kyawun tayu.

Kotu ta jaddada karfin ikon FRSC na hukunta masu abin hawa
Hukumar Kiyaye Hadura Ta Kasa (FRSC). Hoto: PM News.
Asali: Facebook

Benson ya maka hukumar a babbar kotun jihar Akwa Ibom inda ya kalubalanci ikon hukumar na kama motarsa da cin taranshi, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Dahiru Yellow Ya Shaki Iskar ’Yanci Bayan Shekaru 7 A Gidan Kaso Kan Zargin Safarar ’Yar Bayelsa Tare Da Musuluntar Da Ita

Alkalin kotun ya yi fatali da karar Benson akan hukumar FRSC

Benson ya ce hakan take hakkinsa ne inda ya bukaci da hukumar ta biya shi diyyar N10m kan barnar da aka yi masa, cewar rahotanni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin kotun, Aniekan Akpan ya yi fatali da karar inda ya ce hukumar tana da ikon kama abin hawa da kuma cin tarar wadanda suka saba doka.

Benson daga bisani ya daukaka kara zuwa wata kotu da ke Calabar don bi masa kadunsa.

Kotun ta ce hukumar ta na da damar hukunta masu laifi akan hanya

Yayin da yake karanta hukuncin a madadin sauran lauyoyin, Mai Shari'a B. B Aliyu ya ce:

"Hukumar FRSC ta na da damar kamawa da kuma hukunta masu abin hawa kamar yadda doka ta tanadar.
"Mun tabbatar da hukuncin wannan kotun, kuma wannan karar ba ta da madogara."

Kara karanta wannan

Kano: NDLEA Ta Kama Mutum 1,064, Ta Kwace Tan 7.5 Na Miyagun Kwayoyi

Kotun ta kuma kori bukatar Benson na cewa hukumar ta biya shi N10m kan barnar da aka masa, amma sai kotun ta biya hukumar N50,000.

Cire Tallafi: FRSC Ta Shawarci 'Yan Najeriya Su Koma Amfani Da Kekuna

A wani labarin, Hukumar FRSC ta shawarci 'yan Najeriya su koma amfani da kekuna saboda tsadar man fetur.

Hukumar reshen jihar Bayelsa ita ta yi wannan kira inda ta ce amfani da keke na kara lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel