Hukumar FRSC ta kulla wata yarjejeniya da kamfanin Dangote
Hukumar da ke kula da hanyoyi da hana afkuwar hadarurruka (FRSC) da gidauniyar Dangote sun amince da cewar manyan motocin kamfanin ba za su dunga bin hanyoyin kasar ba daga karfe 7:00 na yamma zuwa 7:00 na safe a kullun.
Daga yanzu manyan motocin za su dunga zirga-zirga ne ido na ganin ido kawai.
A Wani jawabi daga Bisi Kazeem, jami’in hulda da jama’a na rundunar a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, ya bayyana cewa wannan yunkuri na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a taron da ya gudana tsakanin kamfanin da hukumar FRSC domin rage afkuwar hadarurruka da motocin.
Hukumar ta kuma bukaci gidauniyar da ta kwashe motocin da suka baci daga manyan hanyoyi akan lokaci.
Oyeyemi ya kuma bukaci kamfanin da ta samar da karin makarantun koyar da tuki sannan kuma a bari ya zama budadde ta yadda direbobi za su iya shiga domin horar da su.
Yace hakan zai tabbatar da tsaro a manyan hanyoyi.
KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta shiga damuwa kan yiwuwar barkewar rikici a lokacin zaben gwamnan Kogi
A cewar Kazeem Shugaban kungiyar ya bayar da wa’adin cika wadannan bukatu ga kamfanin domin rage yawan afkuwar hadarurruka da ya shafi manyan motocinta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng