Kwana 100 a Ofis: Gwamnan Jihar Rivers Ya Kammala Muhimman Ayyuka 21

Kwana 100 a Ofis: Gwamnan Jihar Rivers Ya Kammala Muhimman Ayyuka 21

  • Gwamnan jihar Rivers ya yi bikin cikarsa kwana 100 akan kujerar ta hanyar kammala muhimman ayyuka 21
  • Gwamna Siminalayi Fubara ya kammala ayyukan tituna 21 masu tsawon kilomita 68 a cikin ƙananan hukumomi bakwai na jihar
  • Gwamnan ya kuma fara aikin da babu wata gwamnatin jiha da ta taɓa irinsa a ƙasar nan wanda za a kammala a cikin shekara uku masu zuwa

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da kammala ayyukan tituna 21 masu tsawon kilomita 68 a ƙananan hukumomi bakwai na jihar.

Gwamna Fubara ya kuma samu wasu nasarorin a fannin ilmi, lafiya, jindaɗin al'umma da sauransu a jihar, cewar rahoton Channels tv.

Gwamna Fubara ya yi muhimman ayyuka a jihar Rivers
Gwamna Fubara ya kaddama tituna 21 a jihar Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ce a wani saƙon da gwamnan ya aike da shi wanda aka watsa a gidan talbijin, ya sanar da cewa za a fara ƙaddamar da wasu daga cikin ayyukan a ranar 17 ga watan Satumba, domin murnar cikarsa kwana 100 akan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Kara Farashin Mitar Wutar Lantarki

Nasarorin Fubara cikin kwana 100

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A matsayinmu na gwamnati, babban abin da ya fi muhimmaci a gare mu, shi ne kare rayuka da dukiyoyin al'umma sannan mun yi amanna cewa mun yi ƙoƙarin yin hakan ta hanyar haɗa gwiwa da jami'an tsaro domin samar da zaman lafiya a jihar Rivers."
"A ranar 17 ga watan Yunim 2023, mun ƙaddamar da fara aiki mafi girma da wata gwamnatin jiha ta yi a ƙasar nan, titin zoɓe na Fatakwal a ƙoƙarin da mu ke na gudanar da muhimman ayyuka a jiha."
"Titin mai hannu biyu wanda yake da tsawon kilomita 50.15, idan aka kammala shi a cikin shekara uku masu zuwa, zai haɗa tare da ƙarfaɗa harkokin cigaban tattalin arziƙi a ƙananan hukumomi shida."
"Hakan zai jawo masu zuba hannun jari na cikin gida da waje, wajen zuba jari a fannin gine-gine, noma, kiwon lafiya da masana'antu. Wannan zai ƙara bunƙasa ƙauyukan da ke kan titin su zama birane, samar da ayyukan yi ga matasa da cigaban tattalin arziƙi."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Samu Abinda Yake So, Zai Runtumo Wa Jiharsa Bashin Naira Biliyan 50

Gwamna Oberevwori Ya Ba Abokin Adawa Mukami

A wani labarin na daban, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya ba abokin takararsa a zaɓen gwamna muƙami mai gwaɓi a gwamnatinsa.

Gwamnan ya naɗa Goodnews Agbi wanda ya yi takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP, a matsayin mai ba shi shawara ta musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel