Dalibai Na Da Hannu a Harin Fashi da Aka Kai Dakunan Mata, Gwamnan Ribas

Dalibai Na Da Hannu a Harin Fashi da Aka Kai Dakunan Mata, Gwamnan Ribas

  • Gwamna Fubara ya bayyana waɗanda yake zargi da kai hari ɗakunan ɗalibai mata a jami'ar jihar Ribas
  • Yayin da ya kai ziyara ta musamman jami'ar, gwamnan ya ce baya tunanin wasu 'yan waje ne suka kai farmakin, akwai sa hannun ɗaliban makarantar
  • Ya kara da cewa gwamnatinsa zata yi duk mai yuwuwa ta kamo masu hannu kuma a hukunta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce wadanda suka kitsa harin da aka kai wa ɗakunan ɗalibai mata tare da kwashe wasu kayayyaki a Jami’ar Jihar Ribas da ke Fatakwal daliban makarantar ne.

Fubara ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wata ziyara da ya kai jami’ar, biyo bayan faruwar lamarin da kuma zanga-zangar da dalibai mata suka yi.

Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas.
Dalibai Na Da Hannu a Harin Fashi da Aka Kai Dakunan Mata, Gwamnan Ribas Hoto: Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa ‘yan bindiga da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kai farmaki dakunan kwanan dalibai uku na mata a kusa da kofar shiga jami’ar da safiyar Alhamis.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

Jaridar Punch ta rahoto cewa yayin wannan hari, sun yi awon gaba da kayayyaki masu daraja kamar wayoyin hannu, na'ura mai kwakwalwa da sauransu, sun jikkata mata 4.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamna ya fallasa waɗanda suka kitsa harin

Yayin da yake yin Allah wadai da harin, gwamna Fubara ya ce ya zama dole a kamo wadanda suka kai harin tare da hukunta su.

A rahoton Guardian, gwamnan ya ce:

“A zahirin Gaskiya, na yi baƙin cikin cewa irin wannan abu ya faru a wannan zamanin na mu. Wani ya kutsa kai cikin 'hostel' na ɗalibai mata ya yi lalata da 'yan mata."
"Lokacin da na samu labarin na ce ba kawai zan aika mataimaka na da ’yan sanda bane, da kaina zan zo na ga abubuwan da suka faru kuma na tantance halin da ake ciki."

Kara karanta wannan

Rikicin Nijar: An Fara Fuskantar Karancin Shanu Da Tumaki Bayan Rufe Iyakoki

"Ina mai tabbatar muku cewa dole mu gano tare da cafke masu laifin. Kuma na tabbata ba mutanen waje ba ne. Su ma dalibai ne a nan.”

Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da an kula da daliban da suka samu raunuka a harin tare da bayar da tabbacin daukar matakan da suka dace don hana afkuwar hakan nan gaba.

An Halaka Tsohuwar Shugabar Kotun Kostumare a Jihar Benuwai

Mun kawo muku rahoton cewa an shiga tashin hankali yayin da aka tsinci gawar wata shugabar Alkalai da ta yi ritaya a jihar Benuwai, Misis Margaret Igbeta.

Rahoto ya nuna an gano gawar mamaciyar a gidanta da ke cikin kwaryar birnin Makurdi cikin yanayi mara kyau ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel