Wata Mata Ta Jefa Jaririnta Cikin Kogi a Legas, Ta Bayyana Dalilanta

Wata Mata Ta Jefa Jaririnta Cikin Kogi a Legas, Ta Bayyana Dalilanta

  • Wata mata ƴar Najeriya ta jefa jaririnta cikin kogi a Legas sannan ta yi bayanin dalilin da ya sanya ta yi hakan
  • Kamar yadda aka gani a wani bidiyon da ya yaɗu a soshiyal midiya, wani mutum ya shiga kogin inda ya ceto jaririn
  • A yayin da wasu mutane ke kiran a hukunta ta, wasu sun tausaya mata kan dalilin baƙin cikin da take ciki wanda ya sanya ta aikata hakan

Wani bawan Allah ya ceto wani jariri da mahaifiyarsa ta jefa cikin kogi a kan titin hanyar Badagry a jihar Legas.

Mutane sun taru lokacin da mutumin ya ciro jaririn daga cikin kogin, kamar yadda bidiyon da aka sanya a shafin @lindaikejiblogofficial ya nuna.

Wata mata ta jefa jaririnta a Kogi
Wani bawan Allah ya ceto jariirin daga cikin kogin @Lindaikejiofficial
Asali: Instagram

Matar ta bayyana dalilin jefa jaririn cikin kogi

A cewar @lindaikejiblogofficial, mahaifiyar jaririn ta yi kama da mai cutar taɓin hankali.

Kara karanta wannan

Ruɗani: Matasa Sun Farmaki Wurin Ibada Gami Da Lalata Kayayyaki Da Dama, Bidiyonsu Ya Bayyana

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lokacin da aka tambaye ta dalilin da ya sanya ta jefa jaririn cikin kogin, sai ta ka da baki ta ce ta gaji da rayuwa ne.

Ta ƙara da cewa jaririn ya daɗe a duniya inda har bikin sunansa aka yi, don haka zai iya barin duniya.

Legit.ng ta fahimci cewa an garzaya da jaririn zuwa wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba, domin duba lafiyarsa.

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

chefnshopper ya rubuta:

"Ba hukunci na ke mata ba, amma wannan wani abu ne wanda mata da yawa ke neman samu. Allah ina roƙonka ka cika burin duk matan da ke neman haihuwa musamman waɗanda suka kalli wannan bidiyon suna ji a zuciyarsu yaushe za su samu na su.

officialbolanlebabs ya ributa:

"Dan Allah ko akwai wanda zai iya ɗaukar yaron? Wannan jaririn an ƙaddaro sai ya rayu, kawai dai an haife shi a gidan da bai dace ba ne. Mahaifiyarsa ta iya yiwuwa fyaɗe aka yi mata ko wani abun. A duba lafiyar jaririn sannan a tabbatar an ɗamka shi a hannu nagari. Allah ya albarkaci mutumin da ya ceto shi."

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Ba Da Umarnin Rufe Makaranta Saboda Mummunan Laifin Da Aka Aikata a Cikinta

mamaariella ta rubuta:

"A matsayin wacce ta kwashe shekara 10 tana ƙokarin samun haihuwa ƙafin daga ƙarshe na samu yarona na farko, wannan bidiyon ya sanya ni kuka."

Dan Najeriga Makale a Burtaniya

A wani labarin na daban kuma, wani ɗan Najeriya ya shiga tasku a ƙasar Burtani bayan matarsa ta soke masa biza.

Matar dai ta soke masa bizar ne bayan ya gano tana cin amanarsa da wani daban, inda daga ƙarshe ta rabu da shi ta auri wani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel