Ma’aurata 7 Sun Hada Bikinsu Don Ragewa Juna Zafin Kashe Kudi, Hotunan Sun Yadu

Ma’aurata 7 Sun Hada Bikinsu Don Ragewa Juna Zafin Kashe Kudi, Hotunan Sun Yadu

  • Wasu ma'aurata bakwai daga gundumar Machakos sun gudanar da bikin aure na hadin gwiwa don ragewa juna zafi, suna masu nuni ga matsin rayuwa da ake ciki
  • Sabbin ma'auratan sun kasance dauke da murmushi a fuskokinsu yayin da aka yi shagalin bikinsu sannan sun taka rawar murna kafin suka raba kek
  • Jama'a sun yaba ma masoyan a kan wannan mataki da suka dauka, inda suka karfafa ma sauran jama'a gwiwar yin koyi da su maimakon cin bashi don yin biki

Masu bauta a cocin All Saints Kyamwee Anglican da ke gudunmar Machakos sun halarci wani biki na musamman da ya hada ma'aurata bakwai.

Sun hada bikinsu saboda matsin tattalin arziki
Ma’aurata 7 Sun Hada Bikinsu Don Ragewa Juna Zafin Kashe Kudi, Hotunan Sun Yadu Hoto: ACK Diocese of Machakos.
Asali: UGC

Me yasa ma'auratan suka yi auren hadin gwiwa?

A cewar NTV, ma'auratan sun ce sun yarda su yi biki na hadin gwiwa domin ragewa juna zafi saboda tsadar rayuwa da ake ciki.

Kara karanta wannan

Ruɗani: Matasa Sun Farmaki Wurin Ibada Gami Da Lalata Kayayyaki Da Dama, Bidiyonsu Ya Bayyana

Cocin ya cika makil da yan uwa da abokan arziki da kuma yan cocin da suka hallara domin shaida daurin auren masoyan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ma'auratan sun hallara a coci daya bayan daya yayin da suka baje kolin rawansu masu kayatarwa.

Ma'auratan sun dauki alkawarin aure daya bayan daya sannan suka ciyar da junansu kek da hannayensu.

Daya daga cikin angwanan, Alphonse Mwaziri mai shekaru 74 ya bayyana cewa ya auri kyakkyawar matarsa tsawon shekaru 50.

"Ina zaune da matata cikin farin ciki. Ina rokon wadanda suke cikin zuriyata da su yi koyi da su kuma su yi aure a coci," in ji shi.

Joseph Mutungi, faston da ya daura auren ma'auratan guda bakwai, ya shawarci sauran mutane cewa:

"Kada ku ji tsoron yin aure a coci saboda babu banbanci tsakanin auren coci da na lambu."

Kara karanta wannan

Jami’in Dan Sanda a Adamawa Ya Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Sallame Shi a Aiki, Bidiyon Ya Yadu

Bayan shekaru 3 a Turai, yar Najeriya ta dawo ga saurayinta bakanike

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bakaniken bakin hanya mai suna Segun, ya cika da farin ciki yayin da budurwarsa, wacce ya dauki nauyin karatunta zuwa kasar Birtaniya ta dawo bayan shekaru uku.

Wani mai watsa shirye-shirye a TikTok Theo Ayoms, wanda ya taimaka wajen sake hada su, ya wallafa bidiyon mai tsuma zuciya a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng