'Mu Na Bukatar Karin Jami'ai Dubu 190 Don Kula Da 'Yan Najeriya, Sifetan 'Yan Sanda, Egbetokun

'Mu Na Bukatar Karin Jami'ai Dubu 190 Don Kula Da 'Yan Najeriya, Sifetan 'Yan Sanda, Egbetokun

  • Olukayode Egbetokun, babban Sifetan 'yan sandan Najeriya ya bayyana cewa hukumar su na bukatar karin jami'ai
  • Egbetokun ya ce akalla hukumar na bukatar karin jami'an 'yan sanda dubu 190 don bin ka'idar Majalisar Dinkin Duniya
  • Ya ce a Najeriya ko wane dan sanda na kula da mutane 650 sabanin 460 da Majalisar Dinkin Duniya ta ba da shawara

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Babban Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Olukayode Egbetokun ya ce rashin isassun jami'an 'yan sanda ke kara aikata laifuka a kasar.

Egbetokun ya ce hukumar su na bukatar karin jami'an 'yan sanda akalla dubu 190 don wadatar da tsaro.

Hukumar 'yan ta ce ta na bukatar karin jami'ai dubu 190 don wadatuwar tsaro
Rundunar 'Yan Sanda Na Bukatar Karin Jami'ai Dubu 190. Hoto: @PoliceNG.
Asali: Facebook

Meye sifeta 'yan sanda ya ce?

Sifetan ya bayyana haka ne yayin gabatar da lakca a cibiyar tsare-tsare ta kasa da ke Kuru a jihar Plateau a jiya Laraba 30 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Jami’in Dan Sanda a Adamawa Ya Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Sallame Shi a Aiki, Bidiyon Ya Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Majalisar Dinkin Duniya ta ba da shawarar ko wane dan sanda zai kula da mutane 460, cewar Channels TV.

Amma a Najeriya ko wane dan sanda kula da mutane 650 ne saboda karancin 'yan sanda.

A cewarsa:

"Hukumar 'yan sanda na bukatar karin jami'ai dubu 190 bisa umarnin Majalisar Dinkin Duniya.

Egbetokun ya ce idan har ba a samar da kayan aiki ga jami'an 'yan sanda ba, tabbas gwamnati ba za ta cimma muradun ta ba na habaka tattalin arziki.

Wane shawara ya bayar kan kari 'yan sanda?

Ya kara da cewa:

"Rashin isassun jami'an 'yan sanda zai kawo cikas ga habakan masana'antu a Najeriya.
"Yayin da aka rasa isassun jami'an 'yan sanda a wuraren kasuwanci hakan zai zama barazanar ta yadda bata gari za su kai hari wanda zai gurgunta tattalin arziki."

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari'ar Musulunci Ta Tasa Keyar Bakano Zuwa Gidan Kaso Kan Satar Shanu, Ta Yi Bayani

Bayan haka, ya ce rashin wadatuwar jami'an 'yan sanda ya na da tasiri wurin rashin iya kare kadarorin gwamnati a Najeriya, PM News ta tattaro.

Egbetokun Ya Shiga Ganawa Da Kwamitin Gudanarwa Na Hukumar

A wani labarin, babban Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Olukayode Egbetokun ya shiga ganawar gaggawa da mambobin kwamitin gudanarwa na 'yan sanda.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Egbetokun na ganawar ne da wasu manyan jami'an 'yan sanda a kasar a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel