Ogun: Wani Matashi Ya Halaka Mahaifinsa Mai Shekara 100 Kan N70,000

Ogun: Wani Matashi Ya Halaka Mahaifinsa Mai Shekara 100 Kan N70,000

  • Wani matashi ga zaɓi ya salwantar da rayuwar mahaifinsa mai shekara 100 a dalilin saɓanin da suka samu
  • Matashin dai ya yi iƙirarin ya ba mahaifinsa ajiyar kuɗi har N70,000 amma da ya buƙaci ya ba shi haƙƙinsa sai ya halaka shi
  • Jami'an tsaro dai sun cafke matashin wanda ya amsa cewa.ya aikata laifin halaka mahaifinsa da adda

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ogun - Jami'an tsaro na 'So-Safe Corps' a jihar Ogun, sun cafke wani matashi mai shekara 38 mai suna Mathew Ifeanyi, bisa zargin halaka mahaifinsa, Anthony Nnadike, kan N70,000 da ya ba shi ajiya.

Mathew Ifeanyi dai ya aikata wannan ɗanyen aikin ne a kan mahaifin na sa ne ta hanyar sarinsa da adda, cewar rahoton Daily Trust.

Matashi ya halaka mahaifinsa a Ogun
Matashin ya halaka mahaifin na sa ne da adda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya auku

Kwamandan rundunar tsaron ta So-Safe Corps, Soji Ganzallo, a ranar Laraba ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata a ƙaramar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwan Sani 5 Dangane Da Hambararren Shugaban Kasar Gabon, Ali Bongo

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Ganzallo wani sufetan rundunar mai suna Alabi Gafar wanda yake a ofishin rundunar na Alade/Atago/Ntabo, shi ne ya samu bayanin cewa wani matashi ya farmaki mahaifinsa da adda.

Ganzallo ya cigaba da cewa nan da nan aka aike da jami'ai zuwa wajen da lamarin ya auku domin ceto dattijon, Anthony Nnadike, mai shekara 100, da cafke ɗan na sa.

"Abun takaici, bayan sun isa wajen an garzaya da tsohon zuwa wani asibiti mafi kusa saboda munanan raunikan da ya samu, inda daga baya likitoci suka tabbatar da cewa ya bar duniya." A cewarsa.

An cafke wanda ake zargin

Ganzallo ya bayyana cewa matashin bayan ya ƙi yarda a cafke shi, daga ƙarshe ya shiga hannu sannan aka yi masa tambayoyi.

Ya bayyana cewa a lokacin gudanar da binciken farko, matashin ya bayyana cewa rashin biyansa kuɗinsa N70,000 da yaba mahaifinsa ajiya ne tun ranar 22 ga watan Yunin 2022, ya sanya ya ɗauki wannan matakin.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Daba Da Haɗin Kan 'Yan Sanda Sun Kai Kazamin Hari Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Ɓarna

Matashin ya bayyana cewa ya halaka mahaifin na sa tun da ya ajiye aikinsa domin fara kasuwanci, amma ya ƙi ba shi kuɗinsa.

Kakakin rundunar, Moruf Yusuf, ya bayyana cewa an aike da wanda ake zargin zuwa ofishin ƴan sanda na Sango domin cigaba da bincike da ɗaukar matakin shari'a.

An Daure Masu Satar Motocin Dangote

A wani labarin na daban kuma, kotu ta aike da wasu ɓarayi zuwa gidan gyaran hali bisa satar kayan motocin Dangote a jihar Ogun.

Kotun ta samu ɓarayin su biyu da laifin satar kayan motocin Dangote wanda darajarsu ta kai N976,715.

Asali: Legit.ng

Online view pixel