Edo: Dalibin Jami'ar UNIFORT Ya Daba Wa Budurwarsa Wuƙa Har Ta Mutu

Edo: Dalibin Jami'ar UNIFORT Ya Daba Wa Budurwarsa Wuƙa Har Ta Mutu

  • Jami'an 'yan sanda reshen jihar Edo sun damƙe wani ɗalibain jami'a bisa zargin halaka budurwarsa
  • Wanda ake zargin, ɗan shekara 24 a duniya yana karatu ne a jami'ar Fatakwal (UNIPORT) kuma ya kashe matar da wuƙa
  • Kwamishinan 'yan sanda ya ce nan bada daɗewa ba za a gurfanar da shi a gaban Kotu bisa tuhumar aikata kisan kai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Edo state - ‘Yan sanda a jihar Edo sun kama wani dalibin jami’ar Fatakwal (UNIPORT) mai shekaru 24 wanda ake zargin ya daɓa wa budurwarsa wuka har lahira.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo, Muhammed Dankwara, ya shaida wa manema labarai ranar Talata a Benin cewa mai gidan wanda ake zargin ne ya kai kara ga ‘yan sanda.

Yan sanda sun kama ɗalibin jami'a da ya kashe sahibarsa.
Edo: Dalibin Jami'ar UNIFORT Ya Daba Wa Budurwarsa Wuƙa Har Ta Mutu Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Ya ce Mutumin ya shaida wa ‘yan sanda cewa dalibin ya daba wa matar wuka sau da yawa a wuya da kuma kirji, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Haramun Ne: An Bayyana Babban Matakin da Za a Ɗauka Kan 'Yan Luwaɗi 100 da 'Yan Sanda Suka Kama

Kwamishinan 'yan sandan ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sanda suka kai dauki, inda suka kama wanda ake zargin, suka kwato wukake guda biyu, kana suka garzaya da wacce aka kashe zuwa asibiti, an ajiye gawarta a dakin ajiye gawa."
“Kayan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da wukake guda biyu masu dauke da jini, wayoyin iPhone guda biyu, wayar Nokia daya, kwamfutar tafi-da-gidanka daya, da katin ATM guda biyu."
“An miƙa Kes din ga sashin kisan kai na ɓangaren binciken manyan laifuka na jihar da ke Benin. Za a gurfanar da wanda ake zargi bisa laifin kisan kai nan ba da jimawa ba.”

Meyasa ɗalibin jami'ar ya kashe budurwarsa?

Da yake zantawa da 'yan jarida, wanda ake zargin ya ce budurwar ta taso daga Asaba ta kawo masa ziyara domin jin daɗi tare da shi a Benin a lokacin da ya gano wasu abubuwa a hannunta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: An Kama 'Yan Luwaɗi Sama da 100 Suna Bikin Auren Jinsi a Jiha 1 a Najeriya

Ya ce hakan ne ya haddasa rigima da musayar yawu a tsakaninsu, wanda daga bisani yarinyar ta daɓa masa wuka, kuma ya maida martani ya soka mata wuƙa, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishinan Anambra Ya Bai Wa Yar Sanda Kyautar N250,000

A wani labarin na daban wata 'yar sanda ya samu kyauta mai gwaɓi sakamakon yadda ta ƙi karɓan cin hancin makudan kuɗaɗe a bakin aiki.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Anambra ya yi ƙarin haske kan abinda ya faru har 'yar sandan ta ƙi karban cin hancin da aka mata tayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262