Gabon: Dan Biafra Da Wasu Abubuwan Sani Dangane Da Hambararren Shugaba Ali Bongo

Gabon: Dan Biafra Da Wasu Abubuwan Sani Dangane Da Hambararren Shugaba Ali Bongo

Libreville, Gabon - An sake yin juyin mulki a nahiyar Afirika. Juyin mulkin na ƙasar Gabon shi ne karo na takwas da aka yi juyin mulki a ƙasashe rainon Faransa cikin shekara uku da suka gabata.

Da safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, aka tashi da labarin cewa sojoji sun hamɓarar da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo.

Abubuwan sani dangane da Ali Bongo
Sojoji sun kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo Hoto: Ali Bongo Ondimba
Asali: Facebook

Wasu sojoji a ƙasar ta yankin Afirika ta Tsakiya sun sanar da kifar da gwamnatin Ali Bongo.

Wane ne Bongo? Legit.ng ta yi rubutu kan hamɓararren shugaban ƙasar.

1) Ali Bongo: Ya musulunta

Bongo an haife shi ne da sunan Alain Bernard. Ya samu sunan Ali sannan mahaifinsa ya samu sunan Omar (wanda tsohon sunansa shi ne Albert-Bernard Bongo) a shekarar 1973, bayan shiga musulunci.

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Zayyano Dalilai 4 Da Suka Sanyasu Kifar Da Gwamnatin Kasar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Su kaɗai ne a cikin ahalinsu da suka sauya addini zuwa musulunci.

2) Ali Bongo: Ya gaji mahaifinsa a shekarar 2009

A lokacin mulkin mahaifinsa Omar Bongo, ya yi ministan harkokin ƙasashen waje daga shekarar 1989 zuwa 1991.

Ya wakilci Bongoville a matsayin mataimaki a majalisar tarayya daga shekarar 1991 zuwa 1999, ya yi ministan tsaro daga shekarar 1999 zuwa 2009.

Bayan rasuwar mahaifinsa, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Gabon na shekarar 2009.

3) Ali Bongo: Ya kamu da cutar ciwon sashi a shekarar 2018

Bongo ya kamu da cutar ciwon sashi a watan Disamban 2018, wacce ta sanya aka kwantar da shi a asibiti. Ciwon ya sanya Bongo ya kwashe watanni 10 a gadon asibiti.

4) Ali Bongo: Ya tsallake yunƙurin juyin mulki

A watan Janairun 2019 wasu ƴan tsirarum sojoji sun yi yunƙurin hamɓarar da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Sake Hambarar Da Gwamnatin Farar Hula a Nahiyar Afirika

Sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulkin an aike da su zuwa gidan gyaran hali.

5) Ali Bongo: Asalinsa yana da rudani

Akwai rudani kan asalinsa. Wani ɗan jaridar ƙasar Faransa mai gudanar da bincike wanda ya wallafa littattafai kan tsegumin siyasa, Pierre Péan, ya ce Bongo ɗan Najeriya ne, sannan an ɗauke shi ne a lokacin yaƙin basasar Biafra na 1967-70.

Hamɓarar shugaban dai ya sha musanta waɗannan raɗe-raɗin. Francois Gaulme, wani masanin tarihi ɗan ƙasar Faransa, ya gayawa BBC cewa:

"Ba a fadar shugaban ƙasa a ka haife shi ba. Yana da kusan shekara takwas mahaifinsa ya zama shugaban ƙasa."

6) Iyalan Ali Bongo

Bongo yana auren Sylvia wacce haifaffiyar ƙasar Faransa ce. Yana da ƴaƴa huɗu, mace ɗaya, Noureddin Bongo Valentin, Jalil Bongo Ondimba and Bilal Bongo, waɗanda shi da Sylvia suka karɓi rainonsu a shekarar 2002.

A shekarar 1994, Ali Bongo ya auri matarsa ta biyu mai suna Inge Lynn Collins Bongo, wacce ƴar asalin ƙasar Amurka ce. Ta nemi ya sake ta a shekarar 2015.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Biya Mazauna Abuja Diyyar N825m,.Ya Bayyana Dalili

Kasashen Afirika Da Sojoji Ke Mulki

A wani labarin kuma kun ji cewa akwai ƙasashen Afirika da yawa waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soja.

Ana yawan samun ƙaruwar ƙasashen da ke faɗa wa a ƙarƙashin juyin mulkin soja a nahiyar Afirika. Ƙasar Gabon ita ce ta baya-bayan nan da sojoji suka hamɓarar da gwamnatin farar hula.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng