Wasu Mutanen Kaduna Sun ba Bola Tinubu Sunan Wanda Su ke So Ya Zama Minista

Wasu Mutanen Kaduna Sun ba Bola Tinubu Sunan Wanda Su ke So Ya Zama Minista

  • Wasu daga cikin mutanen Kudancin Kaduna sun ce ba a yi masu adalci idan ana rabon mukamai
  • Shugaban Southern Kaduna Renewed Hope Movement of Nigeria sun roki alfarmar Ministan tarayya
  • Yusuf Kanhu ya roki Bola Tinubu ya nada Dr Abdulmalik Durunguwa ya zama wakilinsu a FEC

Kaduna - Mutanen kudancin jihar Kaduna sun fito su na kokawa kan abin da su ka ce maida su saniyar ware wajen bada mukamai a gwamnatin tarayya.

A ranar Talata ne Daily Trust ta rahoto cewa wata kungiya mai suna Southern Kaduna Renewed Hope Movement of Nigeria ta ce sam ba ayi masu adalci.

Shugaban kungiyar, Yusuf Kanhu ya fitar da jawabi inda ya ce a shekaru takwas da jam’iyyar APC ta yi a mulki, ba a damawa da mutanen kudancin Kaduna.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zaftare Yawan Jami'an Gwamnati Masu Fita Kasar Waje Saboda Rage Kashe Kudi

Minista
Bola Tinubu da Ministocin Najeriya Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

'Yan Kaduna ta kudu su na neman Minista

Yusuf Kanhu ya zargi tsohuwar gwamnatin Malam Nasir El-Rufai da nuna son kai wajen yakin neman zabe, rabon mukamai da raba albarkatun gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutanen kudancin jihar sun zargi tikitin Musulmi da Musulmi da aka fito da shi a zaben 2019 da raba kan mabiya addinin musulunci da kirista a Kaduna.

Kungiyar ta koka da cewa yanzu ko mataimakin gwamnan jiha da aka saba ba su, sun rasa a siyasa.

Minista: Mu na son wakilci a FEC

Saboda haka mutanen yankin su ka kira taron manema labarai, su ka sanar da duniya halin da su ke ciki, zargi ne da gwamnatin baya ta musanya.

Idan an tashi dauko minista da zai wakilci Kaduna a majalisar zartarwa, Southern Kaduna Renewed Hope Movement of Nigeria ta na so a dauko na ta.

Kara karanta wannan

Musulman Kudancin Kaduna Sun Tura Sako Ga Uba Sani, Sun Ce Da Sake A Mukamansa, Bayanai Sun Fito

Rahoton ya ce kungiyar ta kuma roki sabon Gwamna, Uba Sani ya tabbatar ya yi adalci tsakanin al’ummar musulmai da kiristoci wajen raba mukamai.

An kawo sunan Abdulmalik Durunguwa

Idan ba za a iya ba kirista kujerar minista daga jihar ta Kaduna ba, kungiyar ta roki a nada Dr Abdulmalik Durunguwa wanda musulmi ne daga yankinsu.

Dr. Durunguwa kwararren ma’aikaci ne wanda ya rike shugabancin hukumar SEMA, kungiyar ta kuma ce cikakken ‘dan jam’iyyar APC mai mulki ne shi.

Canji a majalisar APC NWC bayan nada Ministoci

Hon Ali Bukar Dalori ya samu kujera a NWC, shi da Mary Idele ne su ka canji Abubakar Kyari da Betta Edu sakamakon ba su kujerar ministoci.

Tsohon ‘dan majalisa, Garba Datti Muhammad ya canji Salihu Lukman, sai aka ji labari Farfesa Abdul Karim Kana ne mai bada shawara kan shari’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel