Musulmai A Kudancin Kaduna Sun Koka Kan Nuna Wariya A Mukaman Gwamna Uba Sani

Musulmai A Kudancin Kaduna Sun Koka Kan Nuna Wariya A Mukaman Gwamna Uba Sani

  • Kungiyar matasa Musulmai daga Kudancin Kaduna sun koka kan yadda aka nuna musu wariya a mukaman Gwamna Uba Sani
  • Sakataren kungiyar, Shu'aibu Abdallah shi ya bayyana haka a jiya Lahadi 28 ga watan Agusta a Kaduna
  • Ya ce Musulman Kudancin Kaduna gaba dayansu APC su ka zaba duk da kalubalen da su ke fuskanta a yankin

Jihar Kaduna - Al'ummar Musulmai daga Kudancin Kaduna sun koka kan yadda Gwamna Uba Sani ya nuna musu wariya a mukamai.

Kungiyar Matasa ta Kudancin Kaduna (MYFOSKA) ta koka yadda Musulmai a sauran bangare su ka samu mukamai duk da cewa sun zabi jam'iyyar adawa ta PDP.

Musulmai Kudancin Kaduna sun koka kan nuna wariya a mukaman Uba Sani
Kungiyar Musulmai A Kudancin Kaduna Sun Koka Kan Nuna Wariya A Mukamai. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Meye Musulmai ke cewa ga Uba Sani?

Sakataren kungiyar, Shu'aibu Abdallah shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 28 ga watan Agusta, cewar PM News.

Kara karanta wannan

Yadda Ganduje Ya Dawo Cikin Lissafin Siyasa, Ya Wargaza Kawancen Kwankwaso-Tinubu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce duk da cewa musulmai a kudancin Kaduna sun zabi APC mai mulki amma ba su samu mukamai daga gwamnatin jihar ba.

Abdallah ya bayyana cewa Musulmai a Kudancin Kaduna sun zabi APC gaba dayansu wadanda su ka kai kashi 40 na masu zabe a yankin.

Ya roki Gwamna Uba Sani da ya taimaka ya saka su a cikin ayyukan samar da ci gaba a jihar.

Meye bukatun Musulmai ga Uba Sani?

Ya bayyana yadda Musulman Kudancin Kaduna duk kalubalen da su ke fuskanta, su ka zabi jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa da na gwamna.

Abdallah wanda ya samu wakilcin Musa Dahiru ya ce sun tabbatar da adalcin jam'iyyar APC wurin sakawa wadanda su ka sha mata wahala a zabubbuka.

Ya ce:

"Mukamai da aka raba sun nuna tsantsar wariya ga Musulmai a Kudancin Kaduna.

Kara karanta wannan

Nasara a Kotun Zabe: Kwankwaso, Abba Gida Gida Da Wasu Jiga-Jigan NNPP Sunyi Taron Addu’a Na Musamman a Kano

"Amma kuma sauran Musulmi a wasu yankuna sun samu mukamai da yawa duk da kin zaban APC da su ka yi.
"Ya kamata mukamai a Kudancin Kaduna na Musulmai ya yi dai-dai da gudumawar da su ka bayar a zabe."

Ya kara da cewa daga cikin mukamai 17 na Uba Sani, uku ne kawai aka bai wa Musulmai 'yan Kudancin Kaduna, cewar The Sun.

El-Rufai Ya Koka Kan 'Yan Kudancin Kaduna

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana yadda masu ruwa da tsaki a Kudancin Kaduna su ke yaki da mataimakansa.

Ya ce hakan na faruwa ne saboda ya ki bai wa wadanda su ke so mukamin mataimakin gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel