Tinubu Ya Rage Yawan Masu Zuwa Majalisar Dinkin Duniya, Ya Bayyana Dalilin Yin Hakan

Tinubu Ya Rage Yawan Masu Zuwa Majalisar Dinkin Duniya, Ya Bayyana Dalilin Yin Hakan

  • Bola Ahmed Tinubu zai hana wasu mukarrabai da jami’an gwamnati zuwa wajen taron UNGA
  • Shugaban Najeriyan ya fitar da wannan umarni ta bakin hadiminsa a makon nan, Ajuri Ngelale
  • Mista Ngelale ya nuna gwamnatin kasar ta na neman hanyar da za a rage facaka da baitul-mali

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya umarci ma’aikatar harkokin kasar waje ta hana fitar da biza ga wadanda ke son halartar taron UNGA babu dalili.

Rahoton da Tribune ta kawo a ranar Litinin ya ce shugaban kasar ya na son dakatar da jami’an gwamnati da babu abin da za su yi a taron da za ayi.

Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a makon nan.

Kara karanta wannan

Ba Za Ta Yi Wu Ba: Tinubu Ya Bayyana Tsari 1 Na Buhari Da Ba Zai Cigaba Da Shi Ba

Shugaba Tinubu
Shugaban Najeriya a taro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Mista Ajuri Ngelale ya ce an dauki wannan mataki ne domin rage facaka da kudin gwamnati, cikakken jawabin ya fito a shafin shugaban kasa a X.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya ce a takaita bada biza

A umarnin da Mai girma Bola Tinubu ya bada, sanawar ta ce ya bukaci ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bi ka’ida wajen bada takardun biza.

Ana so ofishin jakadancin ya bada damar fita kasar wajen ne ga jami’an da sunansu ya fito cikin wadanda majalisar dinkin duniya ta san da zamansu.

Tinubu ya ce mutanen kasar nan sun sadaukar da kai saboda haka ya kamata gwamnatin tarayya ta bi sannu wajen yadda ta ke kashe dukiyarsu.

Umarnin Shugaba Tinubu - Ngalele

"Da wannan umarni na shugaban kasa, an umarci duka ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya da su ke cikin tawagar UNGA su tabbatar da sun takaita adadin hadimai da ma’aikatan da za su je wajen taron.

Kara karanta wannan

"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

A inda aka samu kari ko abin da ba daidai ba, za a cire sunayensu a lokacin tantancewar karshe.
Shugaban kasar ya na so ya tabbatar da cewa daga yanzu, kudin da ake batarwa a kan gwamnati da jami’anta zai yi daidai da tsantseni da sadaukarwar da masu kishin kasa su ka yi a fadin Najeriya."

- Ajuri Ngelale

Yakin Nijar da ECOWAS

An ji labari Naja’atu Muhammad ta na da ja game da yakar Nijar, ta na ganin an saba ka’idojin damukaradiyyar da ECOWAS ta ke so a dawwamar.

Tun can Naja’atu Muhammad ba ta yarda da kamun ludayin Bola Ahmed Tinubu, har gobe ta na ganin shugaban bai nufin yankin Arewa da alheri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel