An Sanya Dokar Hana Hawa Babura Da Kurkura Da Daddare a Kananan Hukumomi 19 Na Katsina

An Sanya Dokar Hana Hawa Babura Da Kurkura Da Daddare a Kananan Hukumomi 19 Na Katsina

  • Saboda yawaitar ayyukan 'yan ta'addan daji da masu garkuwa da mutane, gwamantin Katsina ta sanar da sabuwar doka
  • Dokar za ta hana masu babura da 'yar kurkura zirga-zirga daga ƙarfe 8 na dare zuwa 6 na safe
  • Kananan hukumomi 19 na jihar da matsalar tsaro ta fi ta'azzara a cikinsu ne wannan doka ta shafa

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda, ta sanar da hana hawa babura a ƙananan hukumomi 19 na jihar.

Kwamishinan tsaron gida da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Alhaji Nasiru Mu'azu ne ya bayyana hakan kamar yadda PM News ta wallafa.

Gwamnatin Katsina ta sanya dokar hana hawa babura da kurkura a jihar
Gwamnatin Katsina ta sanya dokar hana hawa babura da kurkura da daddare a jihar. Hoto: Isah Miqdad AD Saude
Asali: Facebook

Dalilin hana hawa babura da kurkura a jihar Katsina

Sanarwar ta ce dokar hana hawa baburan za ta riƙa aiki ne daga ƙarfe 8 na dare, zuwa kare 6 na safe a ƙananan hukumomin 19 da abinda ya shafa.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Zariya, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙananan hukumomin da aka sanya wannan doka dai sun kasance suna fama da matsanancin rashin tsaro na hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Ƙananan hukumomin da dokar ta shafa sun hada da Sabuwa, Dandume, Funtua, Faskari, Bakori, Kankara, Danja, Kafur, Malumfashi, Musawa, Matazu, Danmusa, Safana da Dutsinma.

Ƙarin ƙananan hukumomin su ne Kurfi, Charanchi, Jibia, Batsari da ƙaramar hukumar Kankia.

'Yan sanda sun yi artabu da 'yan bindiga a jihar Katsina

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan batakashin da aka yi tsakanin dakarun rundunar 'yan sandan jihar Katsina da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne.

A yayin artabun, 'yan sandan sun yi nasarar kuɓutar da wani dattijo tare da samun nasarar ƙwato shanu masu tarin yawa da babura daga hannun 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Sauki Ya Zo: Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Abun Alkairin da Zai Faru Kan Man Fetur a Karshen 2023

'Yan ta'addan sun taho da dabbobin da kuma mutumin ne daga wani ƙauye da ke a ƙaramar hukumar Malumfashi da ke jihar ta Katsina.

Masu garkuwa sun sace mutane biyu a Zariyagarkuwa sun sace mutane biyu a Zariya

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sace mutane biyu da wasu masu garkuwa da mutane suka yi a cikin garin Zariya ta jihar Kaduna.

Masu garkuwar sun kawo farmakin ne da misalin ƙarfe 9 na dare a unguwar Wusasa da ke Zariya, inda suka yi harbe-harbe kafin daga bisani su wuce da mutane biyu 'yan uwan juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel