Tinubu Ya Na Tafka Babban Kuskure Wajen Kinkimo Yaki da Nijar Inji Kawu Sumaila

Tinubu Ya Na Tafka Babban Kuskure Wajen Kinkimo Yaki da Nijar Inji Kawu Sumaila

  • Abdulrahman Kawu Sumaila ya na ganin an ci zarafin damukaradiyya idan aka yaki kasar Nijar
  • Sanatan ta ce doka ta wajabtawa shugaban kasa neman izinin majalisa kafin a iya shiga wani yaki
  • Sanata Sumaila ya ce ba za su amince Najeriya ko ECOWAS ta aika dakarunsu zuwa Nijar ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Abdulrahman Kawu Sumaila bai goyon bayan Najeriya ko kungiyar ECOWAS ta aukawa kasar Nijar da yaki a dalilin juyin mulkin sojoji.

Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi magana a wajen wani taro da AIT ta rahoto, a nan ya yi bayanin illar a tura dakarun sojoji zuwa Nijar.

Abdulrahman Kawu Sumaila ya shaida cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu bai nemi izini a hukumance daga majalisa domin a shiga yaki ba.

Bola Tinubu
Shugaban ECOWAS, Bola Tinubu Hoto: @nnpclimited
Asali: Twitter

A lokacin da shugaban kasa yake kokarin tabbatar da mulkin hula a makwabta, sanatan ya zargi shugaban da sabawa ka’idar mulkin farar hula.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Ribadu, Abdussalami kan Yakin ECOWAS a Nijar

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun da Najeriya ta na bin damukaradiyya da ta san da zaman kundin tsarin mulki ne, Sahara Repoters ta ce sanatan ya soki matsayar Tinubu.

"Akwai tafka da warwara a ECOWAS. Su kungiyar (ECOWAS) su na can za su kare damukaradiyya.
Ba haka su ke fada ba? Damukaradiyya mulki ne na tsarin mulki. Mu na da gwamnati mai amfani da tsarin mulki.
Mu Sanatoci a kundin tsarin mulkin Najeriya, mu ke ba shugaban kasa izinin ayi yaki. Ba a tura da bukatar nan ha yau ba.

- Abdulrahman Kawu Sumaila

Juyin mulki ya ci karo da juyin mulki

A rahoton da aka samu daga Daily Nigerian, Sanatan kudancin Kanon bai ganin marabar abin da sojoji su ka yi a Niamey da yunkurin na Najeriya.

"Saboda haka za mu ga abin da za su iya yi. Idan su na kukan sojojin Nijar sun sabawa tsarin mulki

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Da Gaske Janar Tchiani Ya Kira Gwamnatin Tinubu Da haramtacciya? Gaskiya Ta Yi Halinta

Idan ECOWAS da Bola Ahmed Tinubu su ka shiga yaki ba tare da sahhalewar majalisar tarayya ba, wani juyin mulkin aka yi wa farar hula."

- Abdulrahman Kawu Sumaila

Da aka tambaye shi ko za su goyi bayan a tafi yaki idan wasikar shugaban kasa ta iso zauren majalisar dattawa, sanatan ya ce ba za su amince ba.

"Haka kurum ka yi azarbabin yaki da Nijar"

Kun ji cewa Naja’atu Muhammad ta na da ra’ayin cewa ba Nijar ake yaka ba, Najeriya ake yaka domin Bola Tinubu bai taba boye kiyayyarsa ga Arewa ba.

‘Yar siyasar ta ce sojojin da fiye da shekaru 20 sun gaza maganin ta'addanci a Najeriya ba za sui ya zuwa wata kasa kuma ba su da izinin shiga yaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel