Peter Obi, Saraki, Umahi Da Sauransu Sun Halarci Bikin Dan Ekweremadu a Abuja

Peter Obi, Saraki, Umahi Da Sauransu Sun Halarci Bikin Dan Ekweremadu a Abuja

  • Manyan yan siyasa sun halarci shagalin bikin Lloyd, dan Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa
  • Peter Obi, David Umahi, Bukola Sraki, David Mark suna daga cikin manyan masu fada aji da suka halarci bikin
  • An yi shaglin bikin ne a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta, a cocin Basillica of Grace Anglican a Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, tsoffin shugabannin majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim, David Mark da Bukola Saraki sun halarci daurin auren Lloyd, dan Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa a Abuja.

An daura auren Lloyd da Tiffany a cocin Basillica of Grace Anglican da ke yankin Gudu, a babban birnin tarayya Abuja, jaridar The Cable ta rahoto.

Manyan yan siyasa a wajen bikin dan Ekweremadu
Peter Obi, Saraki, Umahi Da Sauransu Sun Halarci Bikin Dan Ekweremadu a Abuja Hoto: Anthonia Ohaso Ihuigwe
Asali: Facebook

Manyan yan siyasa sun halarci shagalin bikin dan Ekweremadu a Abuja

Kara karanta wannan

DSS Sun Cafke Shugaban NSPMC da NIRSAL da ya yi takarar Gwamnan Katsina

Sauran mutanen da suka halarci bikin sun hada da Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Dino Melaye, tsohon sanata kuma dan takarar gwamnan jihar Kogi da David Umahi, zababben minista da sauransu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Auren na zuwa ne watanni uku bayan an yankewa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa,m Ekweremadu da matarsa, Beatrice hukunci a kasar Birtaniya kan safarar sassan jikin dan adam.

An yankewa Ekweremadu shekaru tara da watanni takwas a gidan maza yayin da matarsa ta samu shekaru hudu da watanni shida a gidan yari.

An nada dan Ekweremadu, a matsayin kwamishina

Mun ji a baya cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya zabi Lloyd Ekweremadu a matsayin daya daga cikin kwamishinoni 15 a jihar.

Mbah ya kuma zabi Ada Chukwu, diyar tsohon gwamnan jihar, Sullivan Chime cikin majalisar kwamishinonin sa.

Kara karanta wannan

El-Rufai, Abba Gana: Cikakkun Sunayen Ministocin Babban Birnin Tarayya Tun 1999

SERAP ta nemi Tinubu ya hana Wike, Gaidam da sauransu cin fansho

A wani labari na daban, mun ji cewa kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da Ma'aikatun gwamnati (SERAP), ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da ministocinsa, wadanda suka kasance tsoffin gwamnoni daga karbar kudin fansho daga jihohinsu.

Kungiyar mai zaman kanta ta yi kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na shoshiyal midiya wato Twitter a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel