Dan Fashi Ya Kama Sunan Wani Sifetan 'Yan Sanda a Matsayin Wanda Ke Ba Su Bindigu a Ogun

Dan Fashi Ya Kama Sunan Wani Sifetan 'Yan Sanda a Matsayin Wanda Ke Ba Su Bindigu a Ogun

  • Wani dan fashi da makami da aka kama a jihar Ogun, ya bayyana yadda suke samun makamai
  • Dan fashin mai suna Owonikoko, ya ambaci sunan wani sifetan 'yan sanda da ya ce shi ke ba su bindigu
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin 'yan sandan jihar ta Ogun, bayan kamoshi da aka yi a wani samame

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ogun - Wani dan fashi da makami mai suna Akeem Owonikoko, ya bayyana cewa wani sifetan 'yan sanda mai suna Ola ne yake kawo musu bindigun da suke amfani da su.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi, kamar yadda aka wallafa a shafin Channels TV.

Dan fashi ya fadi wanda ke kawo musu bindigun a jihar Ogun
Dan fashi ya ce wani sifetan 'yan sanda ne ke kawo musu bindigu. Hoto: Native Reporters
Asali: Facebook

Yadda 'yan sanda suka kama dan fashin

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

An kama Owonikoko ne a babbar hanyar Sagamu zuwa Ijebu Ode, a wani samame da kwamandan yankin Ijebu Ode, ACP Omosanyi Adeniyi ya jagoranta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ga wanda ake zargin da misalin ƙarfe 12:30 na dare a cikin wata mota kirar Toyota Camry, yana tunkarar yankin na Ijebu-Ode.

Sai dai a yayin da shi da jama'arsa suka yi arba da jami'an 'yan sanda, sai suka juya akalar motar zuwa kan babban titi, inda daga bisani suka bar motar suka runƙaƙa cikin daji.

Sai dai a yayin da 'yan sanda suka tsananta bincike a yankin, sun yi nasarar cafke Owonikoko, wanda ya yi basaja da kayan 'yan sintiri.

'Yan sanda sun samu bindigu da motoci a wurin dan fashin

Bayan kama Owonikoko, jami'an 'yan sandan sun bincike motarsa inda suka samo kayayyaki na laifi da dama kamar yadda The Eagle Online ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci, Matarsa Da Yara 2, Ciki Harda Jaririn Kwana Daya

Daga ciki akwai wata bindiga ƙirar gida da kuma harsasai mabanbanta sama da guda 100.

A yayinda jami'an 'yan sanda suka isa gidan ɗan fashin, sun bincike shi inda suka gano ƙarin wasu manyan makamai, motoci da kuma miyagun kwayoyi.

Direban mota ya fadi abinda ya sa ya faɗa harkar fashi da makami

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani matashin direba da ya bayyana yadda cire tallafin man fetur ya sanya shi aikata fashi da makami.

Ya bayyana hakan ne a yayin da ya zo hannu, bayan ɗaya daga cikin fasinjojin da ya taɓa yi wa fashi ta gane shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel