Kwana Daya Bayan Rushewar Masallaci, Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Zariya, Sun Sace Wani

Kwana Daya Bayan Rushewar Masallaci, Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Zariya, Sun Sace Wani

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari yankin Zariya da ke jihar Kaduna a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta
  • Maharan sun halaka wasu mutane biyu a Unguwar Kofar Gayan sannan suka yi awon gaba da mutum daya
  • Zuwa yanzu ba a samu wani rahoto kan lamarin daga bangaren yan sanda ko wasu jami'an tsaro a jihar ba

Zariya, Jihar Kaduna - Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki al'ummar Unguwar Kofar Gayan da ke karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna, inda suka halaka mutane biyu tare da yin garkuwa da wani mutum daya.

Lamarin na zuwa ne kwana daya bayan ruftawar ginin masallacin fadar Zazzau da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Yan bindiga sun kai hari Zariya
Kwana Daya Bayan Rushewar Masallaci, Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 2 a Zariya, Sun Sace Wani Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Aminiya ta rahoto, wata majiya ta tsaro ta ce yan bindigar sun farmaki unguwar ne da misalin karfe 11:00 na dare inda suka dungi harbi lamarin da ya kai ga bindige mutane biyu, sannan suka tisa keyar wani yaro guda.

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram Sun Halaka Mutum 5, Sun Yi Garkuwa Da Mata 7 a Jihar Borno

Yan bindiga na yawan kai hari unguwar Kofar Gayan

An tattaro cewa unguwar Kofar Gayan ta dade tana fama da hare-haren yan bindiga tun a shekarun baya kuma an sha kashe mutane a yankin tare da yi masu dauki dai-dai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya kuma nuna cewa a wannan unguwar ne aka yi garkuwa da wani jami'in hukumar kwastam wanda ya yi kimanin kwanaki 69 a hannun masu garkuwa da shi kafin suka sake shi bayan sun karbi kudin fansa.

Majiya ta bayyana wadanda aka kashe a matsayin Shamsuddeen na gidan Larabawa da kuma Shafi’u na gidan Malam Yusuf, dukkansu mazauna unguwar ne.

Har ila yau, majiyar ta ce yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wani yaro mai suna Hamza Auwal, kafin daga bisani jami’an tsaro suka sami nasarar kubutar da shi.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji Sun Ceto Mutane 10 Da Aka Sace Bayan Ajalin 'Yan Bindiga 3, Rundunar Ta Yi Bayani

Ba a ji daga yan sanda ba

Sai dai kuma, zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalinge ba domin wayoyinsa basa zuwa.

Boko Haram sun farmaki Borno, sun kashe fasinjoji da sace mata

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu da ake zaton yan ta'addan Boko Haram ne sun farmaki wasu ayarin motoci dauke da kayayyaki da fasinjoji a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, inda suka kashe mutum biyar da sace mata bakwai, rahoton Ripples Nigeria.

Sun kai hari ne a ranar Alhamis a kan ayarin motocin jami’an tsaro da ke raka motocin fasinja da kayayyaki kusa da garin Banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru a karamar hukumar da misalin karfe 2:30 na rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel