Najeriya Na Bin Nijar Bashin Kudin Wuta Naira Biliyan 4 Bayan Kasar Ta Sayi Kashi 60 Daga Kamfanin Wutar

Najeriya Na Bin Nijar Bashin Kudin Wuta Naira Biliyan 4 Bayan Kasar Ta Sayi Kashi 60 Daga Kamfanin Wutar

  • Hukumar Samar Da Wutar Lantarki, NERC ta ce Najeriya na bin Jamhuriyar Nijar bashin da ya kai Naira biliyan 4
  • Hukumar ta ce kashi 60 na wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar na zuwa ne daga Najeriya
  • A shekarar 2022, Nijar ta sayi kashi 60 na wutar lantarki da take samu daga Najeriya wurin wani kamfani da ke samar da wutan

FCT, Abuja - Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Najeriya (NERC) ta bayyana cewa Najeriya na bin kasar Nijar bashin fiye da Naira biliyan 4.

Hukumar ta ce Nijar ta gagara biyan bashin da Najeriya ke binta na wadata su da wutar lantarki na tsawon lokaci, Legit.ng ta tattaro.

Najeriya na bin Nijar bashin kudin wutar lantarki da ya kai N4.22bn
An Bayyana Adadin Kudin Da Najeriya Ke Bin Nijar Bashin Wutar Lantarki. Hoto: Energy Matters.
Asali: UGC

Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Nijar da ke da alhakin biyan kudaden sun yi kunnen uwar shegu da maganan bashin.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Jerin Kasashe 6 Na Afirka Ta Yamma Da ECOWAS Ta Afkawa A Nahiyar, Bayanai Sun Fito

Yaushe aka datse wutar Nijar?

Najeriya ta datse wutar lantarki da take samarwa Jamhuriyar Nijar a makon da ya gabata, cewar Daily Post.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan mataki na zuwa ne bayan sojojin kasar sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

A shekarar 2022, Nijar ta sayi kashi 70 na wutar lantarki a wani kamfanin Najeriya kamar yadda NIGELEC da ke samar da wuta a kasar ya tabbatar.

Don samar da isasshen wutar ga nijar, NIGELEC ya kulla yarjejeniya da kamfanin wuta a Najeriya.

Yaushe Nijar za ta kamala aikin madatsar ruwa?

Kamar yadda aka yi yarjejeniya, Najeriya na samar da wuta ga kasashen Jamhuriyar Nijar Benin.

Madatsar ruwa ta Kainji da ke jihar Niger ita ke samar da wutar lantarki da ake tsakurawa Nijar.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara ce: Naja’atu Ta Tona Dalilin Shugaba Tinubu Na Tsokano ‘Yaki’ Da Nijar

Jamhuriyar Nijar na kokarin karasa madatsar ruwa a kasar nan da shekarar 2025 don rage dogaro da Najeriya wurin samar musu da wutar lantarki.

An Gargadi Tinubu Kan Afkawa Nijar

A wani labarin, an gargadi Shugaba Bola Tinubu kan kai farmaki Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki a kasar.

Babban lauya a Najeriya, Femi Falana shi ya yi wannan gargadi yayin da kungiyar ECOWAS ke shirin afkawa kasar.

Kasar Najeriya na daga cikin kasashen Nahiyar Afirka ta Yamma da ke kokarin afkawa kasar Nijar saboda kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojoji suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel