Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga 10 a Jihar Zamfara

Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Bindiga 10 a Jihar Zamfara

  • Dakarun sojoji sun halaka ƴan bindiga masu yawa a wani sabon artabu da suka yi da su a wani ƙauye a jihar Zamfara
  • A yayin artabun dakarun sojojin na Operation Hadarin Daji sun sheƙe ƴan bindiga 10 tare da ƙwato wasu mutum tara da suka sace
  • Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato makamai masu tarin yawan da tsaɓar a hannun tsagerun ƴan bindigan

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin sashe na 1 na atisayen 'Operation Hadarin Daji' a jihar Zamfara sun halaka ƴan bindiga 10 da ceto wasu mutum tara da aka yi garkuwa da su.

Dakarun sojojin na Forward Operating Base (FOB) a Danmarke sun yi arangama da ƴan bindigan ne a ranar Talata bayan sun samu bayanan sirri kan motsin ƴan bindigan.

Sojoji sun sheke yan bindiga a Zamfara
Dakarun sojojin sun kuma ceto mutanen da yan bindigan suka sace Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A cikin sanarwar da hukumar sojojin ƙasa ta sanya a Twitter wacce Legit Hausa ta ci karo da ita, ta bayyana cewa ƴan bindigan sun taho ne daga jihar Sokoto ta hanyar ƙauyen Gadazaima a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito

Yadda sojojin suka sheke ƴan bindigan

Nan da nan dakarun sojojin suka shirya yi wa ƴan bindigan kwanton ɓauna inda suka kwashe sa'o'i masu yawa suna fafatawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ragargazar da ƴan bindigan suka sha a hannun sojojin ne ya sanya suka ranta a na kare suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.

A lokacin fafatawar ƴan bindiga 10 suka baƙunci lahira yayin da sauran suka ranta a na kare ɗauke da raunikan bindiga a tattare da su.

Haka kuma, a ƙoƙarin guduwa daga azabar da su ke sha a hannun sojojin da yawa daga cikin ƴan bindigan sun nutse a cikin rafi, yayin da aka cafko wasu guda biyu da ransu.

Shin sojojin sun ƙwato makamai?

Dakarun sojojin sun samu nasarar ƙwato makamai masu yawa da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda shida, bindiga guda ɗaya mai jigida ƙirar PKT da ma'ajiyar makamai guda biyar.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: 'Yan Ta'adda Masu Yawa Sun Bakunci Lahira Bayan Artabu Da Dakarun Sojoji a Arewacin Najeriya

Haka kuma sojojin sun ƙwato harsasai masu yawa, wayoyin hannu guda uku, keken ɗinki guda ɗaya da tsabar kuɗi har N2,410,000 a hannun ƴan bindigan.

Sojoji Sun Sheke Shugabannin 'Yan Bindiga

A wani labarin kuma, dakarun sojojin sama sun yi luguden wuta kan sansanin wani gawurtaccen ɗan bindiga a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun samu nasarar halaka gawurtattun shugabannin ƴan bindiga Ado Aliero da Dankarami a farmakin da suka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng