Hadimin Atiku Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Tinubu Yake Nada Masu Sukarsa Mukamai

Hadimin Atiku Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Tinubu Yake Nada Masu Sukarsa Mukamai

  • An buƙaci sabon shugaban kwamitin sake fasalin haraji, Taiwo Oyedele, da kada ya sauya daga kan gaskiyar da yake a kai
  • Phrank Shuaibu, hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana Oyedele a matsayin mai caccakar shugaban ƙasar ƙafin a ba shi muƙamin
  • Shuaibu ya buƙaci Oyedele da kada ya dai na caccakar tsare-tsaren tattalin arziƙi marasa kyau inda ya zargi Tinubu da yin amfani da salon Sani Abacha wajen janyo ƴan adawa a jikinsa

An caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa naɗin da ya yi kwanan nan na Taiwo Oyedele, wani masani kan haraji a PwC sannan na gaba-gaba wajen caccakar gwamnatinsa.

Phrank Shuaibu, hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, ya ce akwai wata a ƙasa kan naɗin da Tinubu ya yi wa mai caccakar ta sa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Yi Sabon Muhimmin Naɗi a Gwamnatinsa, Bayanai Sun Fito

An caccaki Tinubu kan nadin Taiwo Oyedele
Taiwo Oyedele da Shugaba Tinubu Hoto: PwC, State House
Asali: UGC

Ya bayyana cewa yawan ganawar da Shugaba Tinubu yake yi da ƴan adawa wani shiri ne na kulle musu bakunansu.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A bayyane yake cewa Mr Oyedele yana daga cikin masu caccaka kan sake fasalin haraji. Ranar Asabar ɗin da ta gabata ya nuna wasu kura-kurai kan shirye-shiryen haraji na gwamnatin APC."
"Domin a kulle bakinsa, sai aka naɗa shi shugaban kwamitin sake fasalin haraji a ranar Juma'a, amma ba a sanar da sauran mambobin ba, ƙila suna son ya yi aiki shi kaɗai ne."

An buƙaci Oyedele da kada ya bari Tinubu ya janye masa hankali

Shuaibu ya yi nuni da cewa naɗin da aka yi wa Oyedele ba zai ba shi damar sake yin magana kan wani abu wanda ba daidai ba ne dangane da gwamnatin.

A kalamansa:

"Yakamata Mr. Oyedele ya yi wa kan shi karatun ta natsu kada Tinubu ya shashantar da shi, mutumin da sirrin tagomashin arziƙin da ya samu shi ne yin amfani da kamfanoninsa wajen samar da haraji domin ya samu na shi kason kamar yadda ya yi a Legas."

Kara karanta wannan

Babban Jigon PDP Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Ya Yi Magana Kan Sauya Sheƙa Zuwa APC

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana janyo ƴan adawa cikin gwamnatinsa domin a riƙa mata kallon sahihiyace duk kuwa da dambarwar da ta dabaibaye zaɓen da aka yi masa.

Shuaibu ya ce Tinubu yana kwaikwayon dubarun Janar Sani Abacha, wanda ya raba muƙamai ga masu fafutuka kan zaɓen ranar 12 ga watan Yunin 1993 wanda magabacinsa ya soke.

Shugaba Tinubu Na Shirin Zama Shugaban ECOWAS

Rahoto ya zo kan cewa Shugaba Tinubu na shirin zama shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS).

Shugaban ƙasar zai karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar ne daga hannun shugaban ƙasar Guinea-Bissau, Umaru Sissoco Embolo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel