Jam’iyyar PDP Ta Yi Zaman Gaggawa, Ta Shawarci Shugaba Tinubu Kan Yunkurin Yakar Jamhuriyar Nijar

Jam’iyyar PDP Ta Yi Zaman Gaggawa, Ta Shawarci Shugaba Tinubu Kan Yunkurin Yakar Jamhuriyar Nijar

  • Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya shiga yaki da jamhuriyar Nijar saboda juyin mulkin da aka yi kwanan nan
  • Babbar jam’iyyar adawar ta ce kamata ya yi shugaba Tinubu ya yi amfani da zaman tattaunawa da diflomasiyya a lamarin
  • Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed ne ya bayyana haka bayan ganawarsu a Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan shiga yaki da jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi har aka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki.

PDP ta ce kamata ya yi Tinubu ya watsar da irin wannan bakin tunanin, a maimakon haka ya shiga tattaunawa ta diflomasiyya don cimma nasarar da ake bukata, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shikenan: Sanatocin Najeriya sun yi maganar karshe kan batun tura sojojin Najeriya su yaki na Nijar

PDP ta ja kunnen Tinubu kan shirin yaki da Nijar
Gargadin PDP ga Bola Tinubu | Hoto: @atiku/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Gargadin PDP ga Tinubu

A cewar rahoton Channels TV, Shugaban kungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed, ya bayyana hakan ne bayan wani taron jiga-jigan PDP a Abuja, a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan na jihar Bauchi ya ce:

“Gwamnonin sun shawarci shugaban kasa, babban kwamanda da gwamnatin tarayyar Najeriya da kada su shiga kowane irin yaki da Jamhuriyar Nijar kan juyin mulkin da soji suka yi a kasar a baya-bayan nan, sai dai a yi amfani da duk wani salo na tattaunawa da diflomasiyya.”

Tinubu ya nemi majalisa ta ba shi damar yakar Nijar

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa, Shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, ya rubutawa majalisar dattawan Najeriya wasika game da matakin da kungiyar ta ke shirin dauka kan sojin Jamhuriyar Nijar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar da Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar dattawa wacce ke dauke da takunkumin da aka kakaba wa sojin na Nijar.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fadi Dalilin Ƙin Halartar Taron da Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC

Tun bayan juyin mulkin, ECOWAS ta yi Allah-wadai tare da bayyana matakan da za ta dauka don tabbatar da an dawo da Mohamed Bazoum kan kujerarsa.

Majalisa ta yi watsi da bukatar Tinubu

Sai dai, duk da haka majalisar dattawan Najeriyan ta yi watsi da bukatar Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu saboda wasu batutuwa.

Majalisar ta ce, ba za ta amince a tura sojojin Najeriya su yaki na Nijar ba, amma ta amince da yin Allah-wadai da wannan juyin mulkin.

Ba a kasar Nijar kadai aka fara juyin mulki ba, an sha yi a kasashe da yawa, kuma yanzu haka akwai kasashen da suke hannun soji a nahiyar Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.