Da Dumi-Dumi: Jirgin Saman Max Air Mai Jigilar Alhazan Najeriya Ya Makale a Nijar

Da Dumi-Dumi: Jirgin Saman Max Air Mai Jigilar Alhazan Najeriya Ya Makale a Nijar

  • A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, fadar shugaban ƙasan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa mambobin dogaran dakw tsaron shugaban ƙasa sun yi ƙoƙarin kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum
  • Sa'o'i kaɗan bayan hakan, wasu sojoji sun bayyana a gidan talbijin inda suka yi iƙirarin sun ƙwace mulki a ƙasar ta yankin Afirina ta Yamma
  • Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) tana jigilar Alhazai daga ƙasa mai tsarki, amma juyin mulkin ya ritsa da wasu a Jamhuriyar Nijar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niamey, Nijar - Jirgin saman kamfanin jiragen sama na Max Air mai lamba 5N-ADM ya maƙale a Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da ake yi a ƙasar.

Jirgin saman wanda yake jigilar Alhazan Najeriya daga ƙasa mai tsarki ya maƙale ne dai a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Niamey, rahoton The Punch ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayyar Tinubu Na Ganawar Sirri Da NLC, TUC, Bayyanai Sun Fito

Jirgin Max Air ya makale a Nijar
Jirgin na Max Air yana dauke ne da Alhazai daga kasa mai tsarki Hoto: @MaxAirLtd
Asali: Twitter

Jirgin saman ƙirar b-747-400 ya sauka ne a birnin Niamey da misalin ƙarfe 12:40 na safe inda yake ɗauke da Alhazan Najeriya mutum 360. Kyaftin Maitama shi ne yake jan ragamar jirgin tare da ma'aikata mutum 18.

Sojoji sun hamɓarar da gwamnati a Nijar

Sojojin dake tsaron shugaban ƙasa a Jamhuriyar Nijar sun sanar da kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, a wani juyin mulki da suka yi a ƙasar ta yankin Afirika ta Yamma.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sojojin dai sun kulle shugaban ƙasar ne a fadarsa tare da tsare shi, inda daga bisani suka fito suka bayyanawa duniya cewa sun karɓe ikon mulki a ƙasar.

Tun bayan da sojojin suka tsare shugaban ƙasar dai, ƙasashen duniya suka fito suka fara yin Allah wadai da yunƙurin juyin mulkin da sojojin su ke yi a ƙasar.

Malamin Najeriya Ya Hango Abinda Zai Faru Da Bazoum

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kulle Makarantu Saboda Bullar Cutar Mashako, Ta Bayyana Matakin Dauka Na Gaba

A wani labarin na daban kuma, wani malami a Najeriya ya hango abinda xai faru da shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum.

Malamin ya bayyana hakan ne bayan shugaban ƙasar ya yi iƙirarin cewa Jamhuriyar Nijar na shirin dai na amfani da kuɗin da ƙasar Faransa take buga musu, su koma suna buga na su da kansu.

Malamin ya hasaso cewa a dalilin hakan, ko dai a kashe shugaban ƙasar ko kuma ya fuskanci juyin mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel