Juyin Mulki ko Kashe Shi: Malamin Najeriyan da Ya Gano Abin da Zai Faru da Bazoum

Juyin Mulki ko Kashe Shi: Malamin Najeriyan da Ya Gano Abin da Zai Faru da Bazoum

  • Sojoji sun hambarar da Mohammed Bazoum bayan shekaru biyu ya na kan karagar mulki a Nijar
  • Kafin a kai ga amfani da sojoji wajen kifar da gwamnati, wani malamin Najeriya ya hango hakan
  • Shugaba Mohammed Bazoum ya yi kokarin bijirewa iyayen gidansu watau Faransa da ta raine su

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niger - Wani malamin musulunci, Najeriya, Aliyu Ibrahim Kaduna ya yi magana kwanaki game da abin da yanzu ya faru a Jamhuriyyar Nijar.

An yi hira da Shugaba Mohammed Bazoum, aka ji yana cewa Nijar za ta fara buga kudinta, ta daina dogaro da Faransa da ta mallake su a baya.

Ganin Mai girma Bazoum ya fara kokarin nunawa Duniya za su tsaya da kafafunsu, wannan malami ya yi mummunan hasashe da ya tabbata.

Bazoum
Mohammed Bazoum Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mutuwa ko juyin mulki

A cewarsa, za a nemi ayi wa shugaban kasar makwabtan juyin mulki ko kuwa dai ayi sanadiyyar hallaka shi da sunan an yi hadarin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Bazoum Na Niger Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka Bayan Sojoji Sun Kifar Da Gamnatinsa, Minista Ya Yi Bayani

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Kun fahimci maganar, su na sane wadancan mutanen, saboda haka Shugaban kasar Nijar ya ce kwanan nan za su yarfar da Faransa…
Haba malam! Har yanzu su ke buga maku kudi, kudin da za ku kashe, su ke buga maku, ka yarfar da su? Ko kuwa su yarfar da kai?
Ai yanzu wannan magana da ya fada, ta na can wajen wadanda ta ke. Su na nan, yanzu su na ganin ya za su yi da shi.
To yanzu wannan yaro ya fi karfin uwayen shi, juyin mulki ya dashe da shi ko kuwa a kirkiro masa hadarin jirgin sama.
Meya dace da yaron nan? Malam za su san yadda za su wullar da shi, ka duba Gaddafi.”

- Aliyu Ibrahim Kaduna

Libya: Daga Sahara zuwa lambu

Kamar yadda ya fada a wajen karatu Aliyu Ibrahim Kaduna ya ce haka aka shiryawa Muammar Gaddafi makirci a lokacin yana mulki a kasar Libya.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki

Shehin ya ce a gwamnatin Gaddafi, ‘yan kasar sun samu abinci, gas da kuma saukin rayuwa, amma an yi amfani da mutanensa, har aka ga bayan shi.

Ko da za a harbe Marigayin, malamin ya ce shugaban yana tunanin ba mutanen Libya ba ne su ka yi masa wannan sharri domin su na kaunar sa.

Juyin mulkin Nijar

Duk da an yi kokarin aika dakaru zuwa Nijar, an ji labarin sojoji sun yi juyin mulki kuma sun rufe ko ina domin su hana kasashen waje tsoma baki.

Sau hudu aka yi juyin mulki a wannan kasa ta yammacin Afrika daga shekarar 1960 zuwa yau. Wannan ne zai kasance juyin mulki na biyar a tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel