Likitocin Isra'ila Sun Ceci Rayuwar Suleiman Hassan, Yaro Dan Falasɗinu Da Kansa Ya Kusa Rabewa 2

Likitocin Isra'ila Sun Ceci Rayuwar Suleiman Hassan, Yaro Dan Falasɗinu Da Kansa Ya Kusa Rabewa 2

  • Likitocin ƙasar Isra'ila sun yi nasarar jona kan wani yaro ɗan ƙasar Falasɗin da ya kusa rabewa biyu
  • An bayyana cewa mota ce ta ture Suleiman Hassan, ɗan kimanin shekaru 12 a lokacin da yake a kan kekensa
  • Faruwar hakan ke da wuya sai aka garzaya da shi zuwa wani babban asibitin ƙashi da ke birnin Jerusalem na ƙasar Isra'ila

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jerusalem, Israel - Likitoci a ƙasar Isra'ila sun yi nasarar ceto rayuwar wani yaro ɗan ƙasar Falasɗinu mai suna Suleiman Hassan, ɗan kimanin shekaru 12 bayan mummunan raunin da ya samu.

Daily Mail ta wallafa cewa mota ce ta ture Hassan a lokacin da yake a kan kekensa inda nan take ya samu tsagewa a cikin ƙoƙon kansa da ta kusa raba shi biyu.

Kara karanta wannan

Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanar Cewa 'Yan Najeriya 12m Za Su Rika Samun N8,000 Kowane Wata Har Tsawon Wata Shida, Jama'a Sun Yi Martani

Likitoci sun jona kan yaron da ya kusa rabewa biyu a Isra'ila
Likitocin Isra'ila sun jona kan dan Falasdin Suleiman Hassan da ya kusa rabewa biyu. Hoto: @afshineemrani
Asali: Twitter

Ƙoƙon kan yaron ya kusa rabewa gida biyu

Faruwar hakan ke da wuya sai aka garzaya da shi cikin gaggawa, zuwa wani babban asibiti mai suna 'Hadassah Medical Center' da ke cikin Jerusalem na ƙasar Isra'ila.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A asibitin ne aka gano cewa, jiyojin da suka haɗa ƙoƙon kansa da ƙashin ƙeyarsa sun yi dameji sosai sakamakon bugun da motar ta yi masa.

Hakan ya sanya ƙoƙon kan nasa ya kusa rabuwa da ƙashin da ya haɗa ƙoƙon kan da ƙashin bayansa wanda shi ne ke ɗauke da duk wasu ƙasusuwa da ke kan ɗan adam.

Likitoci sun yi wa yaron aiki cikin gaggawa kuma cikin nasara

Ohad Einav, wanda babban likitan ƙashi ne tare da abokin aikinsa Ziv Asa ne suka gudanar da aikin cikin nasara.

Einav ya ce aikin, wanda ya gudana a cikin watan Yunin 2023, ya basu matuƙar wahala domin kuwa sun shafe sa'o'i masu yawa kafin sun yi nasarar kammala shi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Dau Zafi Kan Kashe-Kashen Da Ake Yi a Jihohin Plateau Da Benue, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni 1

Ya ƙara da cewa nasarar da suka samu wajen ceto rayuwar yaron ta ta'allaƙa ne ga irin ƙwarewar da suka yi a fannin da kuma kayayyakin fasahohin zamani da suka yi amfani da su.

Einav ya kuma bayyana cewa ba ƙaramar nasara ba ce a gare shi ganin cewa yaron ya warke sumul ba tare da samun wata taɓuwa a ƙwaƙwalwarsa ko wani sashe na jikinsa ba.

Tuni aka sallami Hassan daga asibitin, sai dai likitocin za su riƙa duba shi lokaci bayan lokaci har zuwa lokacin da zai kammala warkewa kamar yadda The Times of Israel ta wallafa.

Yajin aikin likitoci ya janyo rasuwar wata mai ciki a Nasarawa

Legit.ng a makon da ya gabata ta kawo muku rahoto kan wata mata mai juna biyu da ta rasa ranta a asibitin kwararru mallakin gwamnatin jihar Nasarawa.

Hakan ya faru ne sanadiyyar rashin likitan da zai duba ta sakamakon yajin aikin da suke gudanarwa a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel