Hadimin Tsohon Shugaba Buhari Ya Bayyana Abubuwan da Tinubu Zai Duba Wajen Nada Ministoci

Hadimin Tsohon Shugaba Buhari Ya Bayyana Abubuwan da Tinubu Zai Duba Wajen Nada Ministoci

  • Wani mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Tolu Ogunlesi, ya lissafo abubuwa shida da ka iya tasiri a wajen nada ministocin Tinubu
  • Kalaman na Ogunlesi sun zo ne kan batun tushen jerin sunayen ministocin da ake sa ran shugaba Bola Tinubu ya yi kuma zai fitar
  • A cewar Ogunlesi, sa'a daya ce daga abubuwan da ke cikin jerin abubuwan da ka iya zama ma’aunin zama minista a mulkin Tinubu

Tolu Ogunlesi, wanda tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, ya fitar da jerin abubuwan da ka iya zama ma’aunin mutanen da za a nada a matsayin ministoci.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya yi tsokaci ne kan tushen jerin sunayen ministocin da ake sa ran shugaban kasa Bola Tinubu ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Nesa Ya Zo Kusa: Shugaban Kasa Tinubu Zai Bayyana Jerin Sunayen Ministocinsa a Wannan Makon, An Yi Karin Bayani

Hanyoyi shida da Tinubu zai bi wajen nada Ministoci
Yadda Tinubu zai nada ministocinsa, inji hadimin Buhari | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Abin da DSS, EFCC suka yi a jerin sunayen ministocin Tinubu

Ogunlesi, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya kamata ‘yan Najeriya su yi tsammanin jerin sunayen ministocin shugaba Tinubu a cikin sabon mako mai zuwa, ya bayyana cewa abubuwa shida ne ke shafar jerin sunayen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da sanyin safiyar Lahadi ne aka bayyana cewa rahotanni daga hukumar DSS da ta EFCC za su tantance irin mutanen da za su shiga cikin jerin sunayen ministocin.

A bisa sabuwar dokar Najeriya, dole ne shugaba Tinubu ya bayyana sunayen ministocinsa tare da mika su ga majalisar dokokin kasar domin tabbatar da su a cikin kwanaki 60na farkon mulkinsa. Ranar Lahadi ce Tinubu ya kwanaki 48 da kama aiki.

Hadimin Buhari ya lissafa abin da zai yi tasiri a jerin sunayen ministocin Tinubu

Kara karanta wannan

Yadda Bincike da Zargin Sata Zai Jawo Na Hannun Daman Tinubu Su Rasa Ministoci

Sai dai Ogunlesi ya yi duba ga wasu fannoni kan abubuwan da suka shafi jerin ministocin.

A cewar Ogunlesi, abubuwa shida ne za su iya tasiri wajen zaban ministocin kuma su ne kamar haka:

  1. Siyasa (tasirin siyasa a lokacin kamfen da kuma a gaba)
  2. CV (kwarewar aiki da gogewa har ma da tarihin ayyukan baya)
  3. Jiha
  4. Addini da jinsi
  5. Abota ta kut-da-kut
  6. Sa'a

Jerin gwamnoni 6 da suka taba yin mataimakin gwamna a jihohinsu

A wani labarin, mai taimaka wa tsohon shugaban kasan ya ci gaba da bayanin cewa sa’a ce kashin bayan komai a wannan jira da ake na ministocin Tinubu.

A siyasar Najeriya, mukamin mataimakin gwamna na zuwa ne da kima da gata da daukaka, amma wasu kadan ne suka samu damar zama gwamnoni jiharsu.

Ga mataimakan gwamnoni da yawa, iyayen gidajensu ba su ganin sun isa su karbi mulki bayan sun yi aiki dasu kafada-da-kafada na tsawon shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Babban Sarki da Tawagarsa a Aso Villa, Bayanai Sun Fito

Duk da haka, wasu kadan sun yi nasarar zama gwamnoni ta hanyar nuna kwazo ko gina kyakkyawar alaka da iyayen gidajen nasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel