Shugaba Tinubu Ya Gana da Mai Martaba Oba Na Benin a Aso Rock

Shugaba Tinubu Ya Gana da Mai Martaba Oba Na Benin a Aso Rock

  • Oba na Benin mai martaba Ewuare II ya ziyarci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock ranar Jumu'a 14 ga watan Yuli
  • Wannan gana wa na zuwa yayin da ake jiran shugaba Tinubu ya tura sunayen ministocin da zai naɗa majalisar tarayya
  • A watan Mayun shekarar da ta shuɗe ne gwamnatin Muhammadu Buhari ta naɗa Oba a matsayin shugaban Open University

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi baƙuncin Oba na Benin, mai martaba Omon’Oba N’Edo Uku’Akpolokpolo Ewuare II a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, D. Olusegun ne ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita ranar Jumu'a, 14 ga watan Yuli, 2023.

Tawagar Oba na Benin ta ziyarci shugaba Tinubu a Villa.
Shugaba Tinubu Ya Gana da Mai Martaba Oba Na Benin a Aso Rock Hoto: DOlusegun
Asali: Twitter

Har kawo yanzun babu cikakken bayani kan dalilin wannan ziyara da babban Sarkin ya kai wa shugaban kasa amma ana hasashen ya je taya shi murna kan karban mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Jiga-Jigai a Villa, Ya Faɗi Yadda Ya Zama Shugaban ECOWAS

Haka zalika ana tsammanin ganawar zata tattauna muhimman batutuwa da suka shafi 'yan Najeriya baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan gana wa na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon sunayen Ministocin shugaban ƙasa, wanda ya karɓi ragamar mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Shugaban kasa na da tsawon wata biyu daga ranar da aka rantsar da shi ya naɗa ministoci kuma ya tura sunayensu majalisar tarayya domin tantancewa.

A watan Mayu FG ya naɗa Oba a matsayin shugaban jami'a

Idan zaku iya tuna wa a watan Mayu, gwamnatin tarayya ta naɗa Oba na Benin a matsayin shugaban jami'ar 'National Open University of Nigeria'.

Mataimakin shugaban jami'ar (VC), Farfesa Olufemi Peters, shi ne ya sanar da haka yayin da majalisar gudanarwan makarantar ta ziyarci Sarkin a Benin City, jihar Edo.

A wancan lokacin, Basaraken ya miƙa godiya ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bisa ganin ya dace kuma ya ɗauko shi ya ba shi wannan mukami.

Kara karanta wannan

Dalla-Dalla: Yadda Dokar Ta Ɓacin da Tinubu Ya Ayyana Kan Samar da Abinci Zata Taimaka Wa Yan Najeriya

Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Aka Nemi Tsige Shugaba Tinubu

A wani rahoton Kotun zabe a Najeriya ta shirya yanke hukunci kan ƙarar APM ta kalubalanci nasarar shugaba Tinubu da Shettima.

APM ta buƙaci Kotu ta soke zaben da Tinubu da Shettima suka samu nasarar zama shugaban ƙasa da mataimaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel