Jerin Ministoci: Shugaban Kasa Tinubu Zai Bayyana Sunayen Ministocinsa a Wannan Makon, Inji Ogunlesi

Jerin Ministoci: Shugaban Kasa Tinubu Zai Bayyana Sunayen Ministocinsa a Wannan Makon, Inji Ogunlesi

  • An rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu yana shirin bayyana jerin sunayen ministocinsa cikin makon nan
  • Tolu Ogunlesi, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci yan Najeriya da su zuba idon ganin jerin sunayen a sabon makon nan
  • A cewar Ogunlesi, za a yi murna a wasu bangarori yayin da wasu za su yi korafi idan aka bayyana jerin sunayen

Rahotanni sun ce Shugaban kasa Bola Tinubu ya shirya bayyana jerin sunayen ministocinsa a makon nan, kuma an yi rabe-raben abun da yan Najeriya za su sa ran gani daga sunayen.

Tolu Ogunlesi, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wata wallafa da ya yi a Twitter a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli, ya bukaci yan Najeriya da su zuba idon ganin jerin sunayen a cikin makon nan mai kamawa.

Kara karanta wannan

Yadda Bincike da Zargin Sata Zai Jawo Na Hannun Daman Tinubu Su Rasa Ministoci

Shugaban kasa Tinubu
Jerin Ministoci: Shugaban Kasa Tinubu Zai Bayyana Sunayen Ministocinsa a Wannan Makon, Inji Ogunlesi Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Abun da zai tabbatar da jerin ministocin Shugaba Tinubu

Ana ta yamutsa gashin baki kan mutanen da za su samu shiga jerin ministocin. Masana harkokin siyasa sun bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta kan irin mutanen da ya kamata shugaban kasa Tinubu ya zaba a majalisarsa, musamman ministoci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A safiyar ranar Lahadi, an bayyana cewa rahotanni daga hukumar DSS da EFCC zai yanke shawara kan irin mutanen da za su samu shiga jerin ministocin.

A bida sabon doka, ya zama dole shugaban kasa Tinubu ya bayyana sunayen ministocinsa sannan ya gabatar da su ga majalisar dokokin kasa domin tabbatar da su cikin kwanaki 60 a ofis. Ranar Lahadi ne ya cika kwanaki 48 da rantsar da shugaban kasar.

Lokacin da shugaban kasa Tinubu zai saki sunayen ministocinsa

Sai dai kuma daga bisani a wannan rana, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Ogunlesi, ya bayyana cewa za a bayyana sunayen ministoci a kowace rana a cikin sabon makon nan mai kamawa.

Kara karanta wannan

Bayan Gana Wa da Tinubu a Villa, Babban Sarki Mai Martaba Ya Aike da Sako Mai Jan Hankali Ga Yan Najeriya

Ogunlesi ya kuma bayyana cewa mutane da dama za su ji takaici, yana mai cewa jihohi da dama sun samu kujera daya ne yayin da wasu suka samu har guda biyu.

Ya rubuta a Twitter:

"Juya ka ce da makwabcinka: BARKA DA MAKON MINISTOCI!
"Idan aka saki jerin sunayen, za a yi murna a bangarori da dama, sannan wasu za su koka.
"Yawancin jihohi za su samu minista daya ne kacal, wasu za su samu biyu. Lamarin kenan. Mutane da dama za su ji takaici."

Kalli wallafar tasa a kasa:

Ministan kudin Tinubu na iya kasancewa tsohon shugaban banki daga kudu maso yamma, majiya

A wani labarin kuma, wata majiya ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu na iya dauko wani tsohon shugaban banki domin ya zama ministan kudinsa.

Hakan na zuwa ne yayin da kallo ya koma sama don ganin wadanda shugaban kasar zai kwaso domin jan ragamar harkoki a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel