Tsohon Shugaban NUC Ya Fadi Dalilin Yin Murabus, Ya Ajiye Mukamin Gwamnati

Tsohon Shugaban NUC Ya Fadi Dalilin Yin Murabus, Ya Ajiye Mukamin Gwamnati

  • Abubakar Adamu Rasheed ya yi bayanin abin da ya jawo aka ji ya bar hukumar NUC haka kurum
  • Shugaban hukumar ta NUC ya ce yana sha’awar ya zama Emeritus a harkar boko, dole ya yi murabus
  • Idan Farfesan ya cigaba da aiki zuwa karshen wa’adinsa, shekarun yin ritaya a jami’a zai kare masa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Abubakar Adamu Rasheed wanda ya sauka daga kujerar hukumar NUC a kan rajin kan shi, ya yi karin haske a kan hikimar barin matsayinsa.

A makon nan ne This Day ta rahoto Farfesa Abubakar Aliyu Rasheed ya na cewa ya bar NUC ne saboda ya zama Emeritus a jami’ar Bayero da ke Kano.

Malamin makarantar ya ce da ya cigaba da aiki a hukumar kula da harkokin jami’o’i ta kasa har zuwa 2026, ba zai iya cin ma wannan dogon buri ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fitaccen malamin addini a Najeriya ya fadi a filin jirgin sama saboda tsananin rashin lafiya

Jami'a
Jami'ar Bayero Kano Hoto: www.buk.edu.ng
Asali: UGC

Farfesan ya bayyana haka da yake mika ragamar shugabancin hukumar da ya jagoranta a wani gajeren biki a hedikwatar NUCa birnin Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abubakar Adamu Rasheed ya gaji?

"An fara nada ni ne Agustan 2016 na tsawon shekaru biyar, da yiwuwar a kara mani wa’adi. An sake nada ni a 2021 na tsawon wasu shekaru biyar.
A lokacin da aka kara mani lokaci a karshen wa’adina na farko a 2021, ba na sha’awar zarcewa.
Har na koma aji a jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), na fara harkar karatu. Ina koyarwa a lokacin da takardar kara mani wa’adin ta fito.
Babu yadda na iya dole in koma NUC. Amma ban taba fadawa Duniya ba. Sai dai na fadawa mai gidana cewa lallai zan koma makaranta.
A jami’ar BUK, ana tsammanin Faresa zai yi ritaya a shekara 70. Amma kafin Farfesa ya zama Emeritus, dolensa ne ya yi ritaya a jami’ar.

Kara karanta wannan

Mutane 6 Sun Rasu a Borno Yayin Da Wani Bam Da 'Yan Boko Haram Suka Binne a Kan Hanya Ya Tashi

Ba za a karbi wata ritaya wajen makaranta ba. Ban kai shekara 70 ba, amma ban so in yi ritaya a inda ba a jami’a ba saboda ina da burin nan.”

- Abubakar Adamu Rasheed

Wanene Emeritus a Farfesoshi?

An rahoto malamin Ingilishin ya na cewa ba za ta yiwu ya cigaba da zama da ‘yan siyasa a Abuja ba, har ya manta cewa shekaru 70 za su cin ma masa.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Emeritus shi ne Farfesa da ya yi ritaya, amma ya cgaba da aikin koyarwa da bincike a jami’a ko da bai karbar albashi.

Shugaban NUC ya yi gaba

A kwanakin baya rahoto ya zo cewa Shugaban hukumar NUC, Abubakar Adamu Rasheed ya rubuta takardar ajiye aiki bayan canjin gwamnati a kasar.

Farfesa Rasheed ya yi shekaru bakawai a kujerar, kuma ya na da ragowar shekaru a ofis amma ya tafi kafin sabuwar Gwamnati ta canza masu rike mukamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel