Majalisa Ta Zargi Muhammadu Buhari, Sanatoci Za Su Binciki Tsohuwar Gwamnati

Majalisa Ta Zargi Muhammadu Buhari, Sanatoci Za Su Binciki Tsohuwar Gwamnati

  • Sanatoci za su fara aiki wannan karo da binciken abubuwan da aka yi a mulkin Muhammadu Buhari
  • Majalisar dattawa ta na zargin akwai abin dubawa a kwangilar da gas da aka ba Acugas Limited a 2017
  • An kuma yi Allah-wadai da yadda aka bi wajen jinginar da tasoshin jiragen saman da ke Abuja da Kano

Abuja - Majalisar dattawa ta ce za ta gudanar da bincike kan kwangilar aikin gas da aka ba kamfanin Acugas Limited a lokacin Muhammadu Buhari.

Abin da ya jawo maganar kuwa shi ne batun da Sanata Aniekan Bassey (PDP, Akwa Ibom) ya kawo a ranar Alhamis, Premium Times ta fitar da labarin.

Aniekan Bassey ya ce a shekarar 2017 ne kamfanin lantarki nan na NDPHC ya shiga yarjejeniyar Dala miliyan 10 da Acugas Limited domin samar da gas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Shafe Harajin da Aka Lafta, Ya Ƙirƙiro Dokokin Rage Raɗaɗi

Majalisa
Za a shiga Majalisar Dattawa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lambar Zainab Ahmed za ta fito?

Wanda ta sa hannu domin a ba kamfanin Calabar Generation Company Limited gas din ita ce Zainab Ahmed, a lokacin ta na Ministar kudi da tattalin arziki.

Sanatan na Akwa Ibom ya ce makudan biliyoyin da aka batar ya jawo abin magana, kuma ana zargin akwai nuku-nuku wajen yadda aka biya kwangilar.

A dalilin haka, rahoton ya ce ‘dan majalisa ya bukaci idan an kafa kwamitin harkar lantarki, a bankado gaskiyar abubuwan da su ka faru wajen wannan aiki.

Za a so majalisa ta gayyaci duk wani ko hukuma da ke da hannu a kwangilar domin a ji ta bakinsu.

Ra'ayin sauran Sanatoci a Majalisa

Sanata mai wakiltar Kuros Riba ta tsakiya, Etang Williams ya nuna yana goyon bayan hakan. Daga baya Sanata Aminu Abass ya ce kudin ya yi yawa.

Kara karanta wannan

TETFund: Bayan Shekaru 10, Sababbin ‘Yan Majalisa Za Su Binciki Gwamnatin Jonathan

Bayan sauraron maganar irinsu Sanata Sampson Akpan (PDP, Akwa Ibom), Barau Jibrin da ya jagoranci zaman ya amince idan an kafa kwamiti, ayi bincike.

Jinginar da filayen jirgin sama

A zaman jiyan ne Aminiya ta rahoto cewa Abdulrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu a majalisa ya kawo batun jinginar da wasu filin jiragen sama.

Sanatan kudancin Kano ya yi tir da yadda aka bada jinginar tashoshin Nnamdi Azikiwe da Aminu Kano a kudi kadan kafin Muhammdu Buhari ya bar ofis.

‘Dan Majalisar ya ce ba a bi ka’ida wajen bada jinginar ba, saboda haka ya bukaci a yi bincike. Nan take Majalisar Dattawan ta amince da maganar da ya kawo.

Gbenga Daniel ya tsaida cin fansho

Rahoton nan ya nuna sabon Sanatan Ogun ta gabas bai da niyyar hada albashin Majalisa da fanshon Gwamna kamar yadda wasu ‘yan siyasa su ke yi.

Gbenga Daniel ya aika takarda zuwa ga Gwamnansa, ya ce a tsaida kudin da ake biyan shi. Fanshonsa a wata ya kai N670,000, sai kuma albashin majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel