Tinubu Bai Nada Hakeem Odumosu A Matsayin Shugaban Hukumar EFCC Ba, Gaskiya Ta Bayyana

Tinubu Bai Nada Hakeem Odumosu A Matsayin Shugaban Hukumar EFCC Ba, Gaskiya Ta Bayyana

  • An karyata batun da ake na cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya naɗa Hakeem Odumosu, AIG mai ritaya, a matsayin shugaban hukumar EFCC
  • Tsohon kwamishinan ‘yan sandan Legas, ya yi watsi da labarin a safiyar Laraba, inda ya ce wasu masu son tada zaune tsaye ne suka ƙirƙiro labarin
  • Jubril Gawat, tsohon mai taimakawa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ne ya ruwaito Odumosu a wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Laraba

Ikeja, Legas - An ƙaryata rahoton da ke cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Hakeem Odumosu, (AIG) mai ritaya, tsohon shugaban ‘yan sandan jihar Legas a matsayin shugaban EFCC.

Jubril Gawat, wanda tsohon mai taimakawa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ne, ya ƙaryata labarin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, kamar yadda ya samu daga tsohon kwamishinan na jihar Legas.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sa Game Da Sabon Sufeto Janar Na 'Yan Sanda, Egbetokun Olukayode

Hakeem Odumosu ya ce ba a nada shi shugaban EFCC ba.
Hakeem Odumosu ya karyat batun nada shi shugabancin EFCC. Hoto: Jubril A. Gawat
Asali: Twitter

Tsohon kwamishinan 'yan sandan ya musanta labarin

A cewar Gawat, tsohon shugaban ‘yan sandan ya ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma wasu masu son tada zaune tsaye ne suka yaɗa shi, don haka ya kamata a yi watsi da shi gaba ɗaya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda ya rubutu a shafinsa na Tuwita:

"Barka da safiya, an cika ni da kiraye-kiraye da saƙonni da dama tsakanin jiya da yau kan wani muƙami na EFCC", ina so in yi amfani da wannan damar wajen karyata wannan labarin, domin kuwa sam ba gaskiya ba ne."

Gawat a yammacin ranar Talata, 21 ga watan Yuni, a wani martani kan wata tambaya a Tuwita, ya ce hukuma ba ta tabbatar da labarin ba saboda haka ba shi da sahihanci.

Shugaba Tinubu bai ayyana Hakeem Odumosu a matsayin shugaban EFCC ba

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sallami Hafsoshin Tsaro da IGP Daga Aiki, Ya Naɗa Sabbin Da Zasu Maye Gurbinsu

Wasu kafafen yaɗa labarai, banda legit.ng, a ranar Talata, sun yaɗa labarin cewa Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas a matsayin shugaban hukumar EFCC, yana jiran amincewar majalisar dattawa a kwanaki masu zuwa.

Duk da haka, babu ɗaya daga cikin rahotannin da ya naƙalto wata hukuma a matsayin tushen labarin.

Idan za ku iya tuna baya, Shugaba Tinubu ya dakatar da tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, Abdulrasheed Bawa, bisa zarge-zargen cin zarafin ofisoshinsa.

EFCC ta saki Samuel Ortom bayan shafe lokaci mai tsawo

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa, tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya samu damar komawa gida bayan shafe fiye da sa'o'i goma yana amsa tambayoyi a ofishin hukumar EFCC.

A safiyar ranar Talata ne dai jami'an hukumar ta EFCC, suka gayyaci tsohon gwamnan zuwa ofishinsu da ke Makurdi babban birnin jihar, domin amsa tambayoyi kan yadda ya gudanar da shekarunsa takwas na mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel