Abubuwan da Ya Dace Kowa Ya Sani Kan Sababbin Shugabannin Soji, IGP da Kwatsam

Abubuwan da Ya Dace Kowa Ya Sani Kan Sababbin Shugabannin Soji, IGP da Kwatsam

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi wa duka hafsohin tsaro masu-ci ritaya, ya nada wadanda za su gaje su
  • A sanarwar da aka fitar daga ofishin SGF, an ji an samu hafsoshin sojoji da wasu manyan jami’an tsaro
  • Mai girma shugaban kasa ya nada sababbin Shugabanni ga hukumar kwastam da rundunar ‘yan Sanda

A ranar Talata, The Cable ta kawo bayani a game da sababbin hafsoshin tsaron da aka nada:

1. Manjo Janar C.G Musa ya gaji Irabor

A ranar Kirismetin 1967 aka haifi C.G Musa a garin Sokoto, said ai iyayensa mutanen Zangon Kataf ne a garin Kaduna, bayan ya girma ya shiga NDA.

Manjo Janar C.G Musa ya rike shugabancin Operation Hadin Kai a shekarar 2021, ya jagoranci yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Janar Taoreed Abiodun Lagbaja: Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Hafsan Sojoji

Shugaban kasa Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya na kallon fareti Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. COAS: Taoreed Lagbaja ya shiga tarihi

Abiodun Lagbaja, Manjo Janar ne da aka haifa a kauyen Ilobu da ke Irepodun a Osun a 1968. Jaridar ta ce ya karanci ilmin wurare, a 1992 ya zama Laftanan.

Lagbaja ya na da digirgir daga makarantar koyon yaki ta Amurka kuma ya rike GOC a Kaduna. Rabon da Bayarabe ya zama COAS tun Alani Akinrinade a 1980.

3. Emmanuel Ikechukwu Ogalla ya zama CNS

Shi ma Emmanuel Ikechukwu Ogalla an haife shi ne a 1968 a Igbo Eze a Enugu. A 1987 ya samu A1 a kowane darasi illa Ingilishi a jarabbawar WASC a NMS.

Haka zalika shi ma ya zama soja ne a shekarar 1992, ya kai matsayin rear admiral bayan kusan shekaru 20. Ogalla ya taba zama Darektan bincike na sojojin ruwa.

Kara karanta wannan

Rusau: NITP Ta Gargadi Gwamnatin Kano Kan Tsagaita Rushe-rushe, Ta Bayyana Irin Asarar Da Aka Tafka

4. HB Abubakar zai shugabanci sojojin sama

A garin Shanono a Kano aka haifi Hassan Bala Abubakar a Satumban 1970. Sabon hafsun ya na cikin wadanda su ka zama sojojin saman Najeriya a Satumban 1992.

Air Wice Marshal HB Abubakar ya rike mukamai da-dama a gidan soja kafin wannan mukami.

5. Emmanuel Undiandeye

Emmanuel Undiandey mutumin Obudu ne a Kuros Ribas. Kwararren soja ne da ya yi aiki har da majalisar dinkin Duniya, kafin zamansa DMI, ya yi aiki a sashen a 2020.

6. Bashir Adewale Adeniyi

Bashir Adewale Adeniyi ya zama shugaban Kwastam, an fi saninsa da Kakakin hukumar. Shi ne jami’in da ya gano $8.07m da za a fita da shi ta filin jirgi a Legas.

Saboda gaskiyar da ya nuna a filin jirgin Murtala Muhammed, aka ba shi lambar MFR.

7. Sabon IGP: Kayode Egbetokun

Kamar yadda aka ji labari, a 1990 Kayode Egbetokun ya fara aikin ‘dan sanda. Ana haka har ya kai matsayin Sufritanda, ya zama babban jami’in tsaron Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

DSS Ta Gano Makuden Kudade A Gidan Emefiele? Gaskiya Ta Bayyana

A lokacin da Tinubu yake gwamna, sabon Sufetan ‘Yan sandan ne ya rike masa CSO. Egbetokun ya yi digirinsa ne a lissafi da kuma digirgir da MBA duk a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel