Jami'an Tsaro Sun Halaka 'Yan Bindiga 5 a Jihar Katsina

Jami'an Tsaro Sun Halaka 'Yan Bindiga 5 a Jihar Katsina

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar kai samame a maɓoyar ƴan bindiga tare da sheƙe biyar daga cikinsu a jihar Katsina
  • Tawagar jami'an tsaro wacce ta ƙunshi ƴan sanda da ƴan sakai tare da mafarauta ta kai samamen ne a ƙananan hukumomin Batsari da Jibia
  • Tawagar jami'an tsaron ta kuma samu nasarar cafke ɗaya daga cikin shugabannin ƴan bindiga da ya addabi yankin

Jihar Katsina - Jami'an ƴan sanda tare da haɗin guiwar ƴan sakai da mafarauta sun halaka ƴan bindiga biyar da cafke ɗaya daga cikin shugabanninsu a jihar Katsina.

Jami'an tsaron sun samu wannan nasarar ne lokacin da suka kai samame ranar Asabar a maɓoyar ƴan bindigan da je a ƙananan hukumomin Batsari da Jibia a jihar Katsina, cewar rahoton Vanguard.

Jami'an tsaro sun halaka yan bindiga a jihar Katsina
IGP Usman Alkali Baba Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Sadiq, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa jami'an rundunar na tawagar hana garkuwa da mutane da na sashin bincike na musamman ne suka jagoranci kai samamen.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojin Sama Sun Soye Kwamandojin ISWAP a Wani Hari Kan Maboyarsu a Jihar Borno

A cewar Sadiq, tawagar jami'an ta tarwatsa maɓoyar ƴan bindiga da dama a ƙauyukan Marake, Garin Yara, da Garin Labo, dukkansu a ƙaramar hukumar Batsari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami'an tsaron sun cafke ƙasurgumin ɗan bindiga

Haka kuma tawagar jami'an ta kai samame tare da tarwatsa maɓoyar wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga, Audu Lankai, wanda ya addabi ƙaramar hukumar Jibia da maƙwabtanta.

Sadiq wanda ya bayyana sunan ɗan ta'addan da aka cafke a matsayin Abubakar Idris, ya bayyana cewa an ƙwato shanu 38, tumakai 40 da awakai 65 a yayin samamen, rahoton Channels tv ya tabbatar.

A cewar kakakin rundunar ƴan sandan jami'ansu na ci gaba da zagaya yankin domin cafke sauran ƴan bindigan da ƙwato kayayyakin da ke hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike.

Legit Hausa ta samo jin ta bakin ɗaya daga cikin ƴan kwamitin tsaro na ƙaramar hukumar Jibia, Mallam Nasiru, wanda ya tabbatar da nasarar da jami'an tsaro tare da haɗin guiwar ƴan sakai suka samu akan ƴan bindigan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Bayan Mahara Sun Halaka Babban Basarake a Arewa Tare Da 'Ya'yansa

Malam Nasiru ya bayyana cewa an faro sharar kakkaɓe ƴan bindigan ne tun daga ƙaramar hukumar Batsari inda aka dangane da ƙaramar hukumar su ta Jibia.

Ya kuma bayyana cewa an samu ci gaɓa sosai sha'anin tsaro a yankin saboda tashi tsaye da suka yi suka haɗa kawunansu domin magance matsalar. Ya kuma yaba wa DPO na Jibia bisa namijin ƙoƙarin da yake yi.

Mahara Sun Halaka Babban Basaraken Fulani

A wani labarin na daban kuma, wasu miyagun mahara sun halaka wani babban basaraken Fulani (Ardo) tare da ƴaƴansa guda huɗu a wani mummunan hari a jihar Kaduna.

Maharan dai sun kai farmakin ne a wani ƙauyen Fulani da ke a ƙaramar hukumar Zaria ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng