Abubuwa 7 da Suka Hana Abdulaziz Yari Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Abubuwa 7 da Suka Hana Abdulaziz Yari Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

  • Siyasar majalisa ta kare, an zabi wadanda za su yi jagoranci bayan makonni ana yakin neman mukamai
  • Akwai abubuwan da su ka yi tasiri a zaben da aka yi, har Godswill Akpabio ya tserewa Abdulaziz Yari
  • An ba tsohon Gwamnan na jihar Zamfara ratar kuri’u 17 a zaben shugaban majalisar dattawa da aka yi

Abuja - A wannan rahoto, Legit.ng Hausa tayi nazarin abubuwan da su ka jawo tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya gagara samun nasara.

Ga wasu daga cikin dalilan da ake gani:

Abdulaziz Yari
Abdulaziz Yari ya rasa zaben Majalisa Hoto: @JamiluSufi
Asali: Twitter

1. Yadda APC ta ware kujeru

Shugabannin Jam’iyyar APC sun yarda cewa shugaban majalisar dattawa ya fito daga Kudu maso kudu, sai a ba Arewa maso yamma kujerar mataimaki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Sanatan APC: Kar Wanda Ya Ga Laifina Idan Sabon Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bai Wa Yan Najeriya Kunya

Abdulaziz Yari wanda ya fito daga yankin Arewa ta yamma ya gamu da cikas tun farko domin idan aka yi wa APC biyayya, Barau Jibrin zai samu mukami.

2. Fadar shugaban kasa

An ji yadda Sanata Ali Ndume ya ke bada labarin irin gudumuwar da Bola Ahmed Tinubu ya bada saboda ganin Godswill Akpabio ya lashe zaben na jiya.

Mai girma shugaban kasa ya yi yadda ya iya har ana gobe zabe domin ganin Yari bai kai labari ba. Ka da a manta, mai dakinsa Sanatar Legas ce tun 2011.

3. Yaushe ka zo Majalisa?

Daga David Mark zuwa Ahmad Lawan, duka shugabannin majalisar da aka yi sun dade kafin su shiga takara, shi kuwa Yari sai yanzu aka rantsar da shi.

Godswill Akpabio ya yi shekara hudu a majalisa, akwai abokan aikinsa a cikin Sanatocin.

4. Kashim Shettima bai tare da Yari

Baro-baro aka ji Kashim Shettima ya fito yana goyon bayan Kiristan kudu a zabe, ya nuna bai dace a sake samun wani Musulmi ya rike mukami na uku a kasar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 11 da Suka Taimaki Tajudden Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

Mataimakin shugaban kasar ya wakilci Borno ta tsakiya, ya sa kan aikin Majalisa.

5. Rasa mulkin Zamfara

Mulkin jihar Zamafara ya bar hannun Jam’iyyar APC a zaben 2023, wannan ya jawo tsohon Gwamnan bai da wanda zai ba shi kwarin gwiwar takara.

Sabon Gwamna, Dauda Lawal Dare ya na mulki ne a PDP, hakan ya jawowa Yari karin matsala.

6. Uzor Kalu da kokarin Hope Uzodinma

Ana tunanin rade-radin hakura da takara da Orji Uzor Kalu ya yi, ya taimaka wajen rage kuri’un da ya kamata Abdulaziz Yari ya samu daga kudu maso gabas.

Idan rahotanni sun tabbata, Gwamnan Imo ya taka rawar gani sosai wajen janye wasu masu goyon bayan Alhaji Yari da farko, su ka zabi Godswill Akpabio.

7. Zargin da ke kan wuyan Yari

Watakila zargin da aka rika jifan zababben Sanatan da shi ya yi tasiri, har ya dage wajen wanke kan shi. An zargi wasu 'yan takaran da amfani da dukiya.

Kara karanta wannan

Godswill Akpabio Ya Doke Abdulaziz Yari, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Shi ma Godswill Akpabio bai rasa kashi a gindinsa, amma kusan babu wanda ke magana a kai.

Ya aka yi Abbas ya yi nasara?

A rahoton da mu ka fitar, kun ji cewa wannan karo fadar shugaban kasa ta tsoma baki a zaben ‘yan majalisar bayan ganin kuskuren da aka tafka a 2015.

Mukhtar Betara, Yusuf Gagdi da Ado Doguwa sun hakura da takararsu, su ka yi mubaya’a ga Iyan Zazzau, hakan ya taimakawa Tajuddeen Abbas PhD.

Asali: Legit.ng

Online view pixel