Yanzu Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Mataimakin Gwamna Douglas Acholonu Ya Mutu

Yanzu Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Mataimakin Gwamna Douglas Acholonu Ya Mutu

  • Al'ummar Imo na cikin alhini yayin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dr Douglas Acholonu, ya kwanta dama
  • Acholonu wanda ya kasance kwararren likita ya mutu a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni kuma za a binne shi a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuni
  • Basaraken masarautar Ishiobiukwu Gedegwum, mai martaba Eze Dr. Patrick Chinedu Acholonu, ne ya sanar da labarin mutuwar yariman

Basaraken masarautar Ishiobiukwu Gedegwum, mai martaba Igwe na Orlu, Eze Dr. Patrick Chinedu Acholonu ya sanar da labarin mutuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Dr Douglas Acholonu.

Acholonu, yarimar masarautar Orlu Gedegwum, ya mutu a safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Yunin 2023, jaridar The Nation ta rahoto.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma
Yanzu Yanzu: Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Tsohon Mataimakin Gwamna Douglas Acholonu Ya Mutu Hoto: Imo State Government
Asali: Facebook

Za a sanar da shirye-shiryen jana'izar tsohon mataimakin gwamnan, Eze Acholonu

Eze Acholonu, wanda ya sanar da labarin mutuwar ta hannun sakataren fadarsa, Dr. Henry Acholonu, ya bayyana marigayin wanda ya kasance kwararren likita a matsayin jigon kasa mai halayan kirki da dattako.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisun Tarayya Na 10, Muƙamai, Da Jihohin Da Suka Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa za a sanar da cikakken bayani game da jana'izarsa yayin da gidan sarautar ke tattaunawa da gwamnatin jihar Imo da kuma cocin Katolika da ke Orlu domin shiryawa marigayin bikin mutuwa na musamman wanda za a yi a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli.

Malami ya ki yi wa jarumin fim addu'a saboda zargin cewa dan gargajiya ne

A wani labari na daban, mun ji cewa an samu cece-kuce a yanar gizo, bayan da wani malamin addinin Islama mai suna Sheikh Yelma’e, ya fito cikin wani bidiyo ya caccaki musulman da suka je jana’izar jarumin fina-finan kudancin ƙasar nan Murphy Afolabi.

Ya bayyana jarumin da cewa munafiki ne (dan gargajiya) ko kuma ma shi yana ganin cewa mai bautar gumaka ne.

A cikin faifan bidiyon da ya karaɗe kafafen sada zumunta, malamin ya bayyana cewa ba zai iya yiwa Murphy addu'a ba saboda irin matsayin da ya ke fitowa a fina-finai, waɗanda galibinsu na addinin gargajiya ne.

Ya kuma kara da cewa irin waɗannan fina-finai sun ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci, a domin haka ne ma ya ke shawartar masana'antar fina-finan Yarbawa da su daina shirya irin waɗannan fina-finai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel