"Ɗan Gargajiya Ne, Ba Musulmi Ba": Wani Malami Ya Ƙi Yin Addu'a Ga Marigayi Jarumi Murphy Afolabi

"Ɗan Gargajiya Ne, Ba Musulmi Ba": Wani Malami Ya Ƙi Yin Addu'a Ga Marigayi Jarumi Murphy Afolabi

  • A cikin makon nan aka yi jana’izar jarumin Nollywood, Murphy Afolabi, wani malamin addinin Musulunci ya ƙalubalanci malaman da suka yi wa jarumin addu'a a wajen
  • A cikin wani faifan bidiyo, malamin ya bayyana Murphy a matsayin kafiri mai bautar gumaka domin a ko yaushe yana fitowa a matsayin ɗan gargajiya ne a cikin fina-finai
  • Sai dai kwanaki kaɗan bayan kalaman malamin da suka jawo cece-kuce, wasu abokan Murphy sun shirya taron addu'ar kwanaki uku ga jarumin da ya rasu

An samu cece-kuce a yanar gizo, bayan da wani malamin addinin Islama mai suna Sheikh Yelma’e, ya fito cikin wani bidiyo ya caccaki musulman da suka je jana’izar jarumin fina-finan kudancin ƙasar nan Murphy Afolabi.

Ya bayyana jarumin da cewa munafiki ne (dan gargajiya) ko kuma ma shi yana ganin cewa mai bautar gumaka ne.

Kara karanta wannan

“Na Haɗa Kayana Na Bar Gidan": Wani Magidanci Yayi Fushi Ya Bar Matarsa Bayan Da Surukarsa Ta Dawo Gidansu

Jarumi Murphy Afolabi
Wani Malami Ya Ƙi Yin Addu'a Ga Marigayi Jarumi Murphy Afolabi. Hoto: @temilolasobola/@olamilekanayinlaagbaye_220
Asali: Instagram

Irin fina-finan sun saɓa da koyarwar musulunci

A cikin faifan bidiyon da ya karaɗe kafafen sada zumunta, malamin ya bayyana cewa ba zai iya yiwa Murphy addu'a ba saboda irin matsayin da ya ke fitowa a fina-finai, waɗanda galibinsu na addinin gargajiya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma kara da cewa irin waɗannan fina-finai sun ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci, a domin haka ne ma ya ke shawartar masana'antar fina-finan Yarbawa da su daina shirya irin waɗannan fina-finai.

Punch ta ruwaito malamin yana cewa da yawa daga cikin jaruman da ke fitowa a irin waɗannan fina-finai, na tunanin cewa wasan kwaikwayo kawai suke yi.

Babu maganar wasa a abinda ya shafi ubangiji

Sai dai ya ce babu batun wasa a cikin lamarin da ya shafi Ubangiji. Ya kuma ce fitowa a matsayin boka, maye ko matsafi duk ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Manyan ‘Yan Siyasar da Ake Tunanin Tinubu Zai Naɗa Ministoci In Aka Rantsar Da Shi

Ya ƙara da cewa shi fa bai ga dalilin da zai sa musulmi ya riƙa kwaikwayon abubuwan waɗanda ba su yi imani ba da sunan nishaɗantarwa.

Ya kuma ƙara da cewar ya na yawan ganin hakan a fina-finan Hausa, Yarbawa da kuma na Inyamurai. Sai dai ya bayyana cewa abin ya fi ƙamari a fina-finan Yarbawa.

Abokan mamacin sun yi masa addu'a

Sai dai kwanaki kaɗan bayan maganganun malamin, wasu daga cikin abokan jarumi Murphy sun yi watsi da kiran da ya yi, inda suka shirya taron addu'o'in kwana uku a gidan jarumin.

Ya ce duk wani jarumi da ya rasu yana irin waɗannan fina-finai to fa bai kamata a tsammaci cewa za su zo su yi masa addu'a ba.

Kalli faifan bidiyon malamin da ya kira Murphy Afolabi da mai bautar gumaka a ƙasa:

Jarumin fim ya burmawa wani wuka kan N1,000

A wani labarin mu na baya, wani jarumin wasan kwaikwayo Temitayo Ogunbusola ya burmawa makwabcinsa wuka da ta yi sanadiyyar ajalinsa kan N1,000.

'Yan sanda sun yi nasarar cafke jarumin tare da gurfanar da shi a gaban kotu don karbar hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel