Baki Ke Yanka Wuya: Kotu Ta Tasa Keyar Mata Zuwa Gidan Kaso Saboda Kiran Kawarta Da Mummunan Suna

Baki Ke Yanka Wuya: Kotu Ta Tasa Keyar Mata Zuwa Gidan Kaso Saboda Kiran Kawarta Da Mummunan Suna

  • Kotun shari'ar Musulunci da ke Kano ta tasa keyar wata matashiya, Habiba zuwa gidan gyaran hali saboda furta kalaman batanci ga kawarta
  • An gurfanar da Habiba bisa zargin kiran kawarta da ta yi a matsayin karuwa a shafin sadarwa ta WhatsApp da kuma tura sakon ga wata kawarta
  • Alkalin kotun, Mallam Sani Tanimu Hausawa ya umarci a tura Habiba zuwa gidan kaso

Jihar Kano - Kotun shari'ar Muslunci da ke zamanta a jihar Kano ta tasa keyar wata mata gidan kaso mai suna Habiba saboda kiran kawarta Rukayya Muhammad a matsayin karuwa.

Kotun shari'ar Musuluncin ta yanke wa wadda ake zargin mai suna Habiba daurin watanni uku a gidan gyaran hali, don gyara halayenta a nan gaba.

Kotu ta tasa keyar mata zuwa gidan kaso saboda kiran kawarta da mummunan suna
Kotu Ta Tasa Keyar Mata Zuwa Gidan Kaso a Kano. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

An gurfanar da Habiba ne a gaban kotun saboda ta kira kawarta da 'Sharmota' wanda ke nufin karuwa a shafin sada zumunta ta zamani na Whatsapp.

Kara karanta wannan

Sabon Yayi: Kotu Ta Tasa Keyar Dan Damfara Zuwa Ofishin EFCC Don Karbar Lakca, Ta Gindaya Masa Ka'idoji

Matar ta tura sakon bata sunan zuwa shafin sadarwar WhatsApp na kawarta da ke Saudiyya

Ta kuma sake tura irin wannan sakon ga wata kawarsu da ke zama a Saudiyya, cewar Daily Trust.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadda ake zargin, Habiba ta amince da aikata dukkan laifukan da kotun ke tuhumarta akai.

Alkalin kotun, Mallam Sani Tanimu ya umarci a tura ta zuwa gidan kaso na tsawon watanni uku

Alkalin kotun, Mallam Sani Tanimu Hausawa ya umarci a tasa keyar Habiba zuwa gidan gyaran hali har na tsawon watanni uku da zabin biyan tara har N40,000.

Har ila yau, Alkalin kotun, Mallam Sani ya umarci wadda ake zargin ta je shafin Whatsapp din ta bayyana wa kawarta da ke Saudiyya cewa karya ta ke yi, ta kuma neman afuwa wurin wadda ta batawa suna.

An Tasa Keyar Matasa 2 Da Suka Ci Kwalan Limamin Unguwarsu Zuwa Gidan Kaso

Kara karanta wannan

Rashin Daraja: DJ Ya Addabi 'Yan Islamiyya da Kida Ya Gamu da Fushin Alkali

A wani labarin, kotun shari'ar Musulunci da ke Kano ta garkame matasa biyu bisa zargin cin zarafin limamin unguwarsu.

Matasan biyu, Adam Yahaya da Muslim Ibrahim sun ci kwalar limamin ne mai suna Mallam Muhammad Auwal Tsamiya don ba sa son ya ci gaba da limanci a masallacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel